An kama Sanatan da ake zargi da karkatar da kudin yaki da korona yana boye kudi 'tsakanin mazauninsa' yayin da 'yan sanda suka kai sumame gidansa

An kama Sanatan da ake zargi da karkatar da kudin yaki da korona yana boye kudi 'tsakanin mazauninsa' yayin da 'yan sanda suka kai sumame gidansa

- An kama wani sanata a ƙasar Brazil da ake zargi da karkatar da kuɗin tallafin korona yana ɓoye takardun kuɗi a tsakanin mazaunansa

- Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 14 ga watan Oktoba yayin wata sumame da ƴan sanda suka kai

- Sanata Chico Rodriguez ya bayyana cewa ƴan sanda sun kai sumame gidansa amma bai faɗi cewa an samu kuɗi tsakanin mazaunansa ba

An kama wani sanata ɗan kasar Brazil yana boye kudi a tsakanin mazaunansa, yayin wani bincike da ƴan sanda ke yi don gano inda aka karkatar da wasu kudade da aka tara don yakar korona a kasar.

DUBA WANNAN: Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

An kama Sanata yana ɓoye takardun kuɗi tsakanin mazaunansa
An kama Sanata yana ɓoye takardun kuɗi tsakanin mazaunansa
Asali: Twitter

Hukumomi sunce sun mamaye gidan Chico Rodrigues a arewacin jihar Roraima, a Brazil, ranar Laraba 14 ga watan Oktoba a wani zargin cin hanci da rashawa.

A yayin samamen, ƴan sanda sun sami kudin da ya 30,000 reais (fiye da £4,100) ruwan kudi, inda aka gano wasu daga cikin kudin a dan kamfen sanatan, wasu ma a tsakanin mazaunansa, wata majiya ta kusa da masu binciken suka tabbatar da hakan.

Ƴan sandan sun ce suna kokarin gano wuraren da aka aikata laifin kwashe kudaden da aka tattara don yakar annobar korona a jihar ta Roraima.

KU KARANTA: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Da yake tabbatar da sumamen Sanata Rodrigues ya bayyana cewa ƴan sanda sun caje shi a matsayin wani matakin bincike wanda ya hada dani, sai dai bai faɗi cewa an samu kuɗi a tsakanin mazaunansa ba.

Ya kuma yi korafin cewa sun zagaye masa gida yayin da yake gudanar da aikinsa a matsayin wakili, kuma ya kara da cewa bashi da hannu a abin da ake zarginsa.

Shugaba Bolsonara ya zargi masu yada labarai da yada jita-jita da kuma dorawa gwamnatinsa laifin cin hanci.

"Wannan bincike misali ne da ke nuni da cewa babu rashawa a gwamnati na, kuma muna yaƙarsa ta ko wanne hali," Bolsonara ya fadi.

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta tsare wani ma'aikacin gidan gyaran hali mai suna Danladi Bako bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin tabar wiwi ce.

Mallakar tabar wiwi laifi ne da aka tanadarwa hukunci a sashe na 19 na dokar hukumar NDLEA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel