Ina neman matar aure amma da sharadin ba zamu haihu ba - Matashi

Ina neman matar aure amma da sharadin ba zamu haihu ba - Matashi

- Duniya juyi-juyi, idan kana da rai za ka ga abubuwa daban-daban suna faruwa

- Yayinda wasu ke addu'a Allah ya basu 'yaya, wani na cewa shi baya son haihuwa

- Ya bayyana tallar neman auren matar da zata iya zama da shi a hakan

Wani matashi ya yi ikirarin cewa yana da ka'idar rashin son haihuwa kuma ya alanta niyyar neman auren duk macen da ta shirya bin ka'idarsa.

Matashin mai suna Abayomi Oluwaseun bai bayyana dalilin da ya sa bai son haihuwan yara ba.

Ya bayyana neman aurensa a shafin ra'ayi da sada zumunta kuma ya ce duka macen da ta shirya ta tuntunbeshi.

Duk da cewa mutane da dama sun bayyana mamakinsu kan wannan irin mutumi, wasu na ganin zabinsa ne kawai.

"Ina neman macen da za ta amince da ka'ida ta na rashin yara. Idan kin amince, yi min magana," Abayomi Oluwaseun ya bayyana.

Wannan talla da yayi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta inda wasu ke cewa da alamun mutumin bai da lafiya yayinda wasu kuma sunce la'alla dan kungiyar asiri ne.

KU KARANTA: Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas

Ina neman matar aure amma da sharadin ba zamu haihu ba - Matashi
Matashin Credit: pusle.ng
Asali: UGC

DUBA NAN: Sojoji sun suburbudi yan sanda masu amsan na goro hannun mutane a kan titi (Bidiyo)

A wani labarin mai tashe, wani fai-fain bidiyon jami'in dan sandan Najeriya ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka gansa yana nadin tabar wiwi a bainar jama'a rike da bindigarsa.

Wannan bidiyon ya bayyana ne lokacin da matasan Najeriya ke zanga-zangan neman sauyi a hukumar yan sandan Najeriya saboda irin cin zarafin da suke yiwa yan Najeriya.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa ire-iren wadannan yan sanda ke kashe matasa bayan sun bugu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel