Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas

Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas

- Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa dalibai 181 na wata makarantar kwana dake Lekki sun kamu da cutar COVID-19

- Farfesa Akin Abayomi, kwamishanan lafiyan jihar ya bayyana hakan da yammacin Juma'a

- Abayomi yace wata dalibar ajin SS1 ta fara rashin lafiya ranan 3 ga Oktoba kuma aka kora ta gida bayan karamin jinya a makarantar

Wani rahoton The Nation ya nuna cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugun cutar Korona.

Legit.ng ta tattaro cewa kwamishanan lafiyan Legas, Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar.

Kwamishanan yayinda yake bayanin binciken, ya ce wata daliba mai shekara 14, yar ajin SS1 ta fara lafiya ranar 3 ga Oktoba kuma aka tura ta gida bayan karamin jinyar da tayi a makarantan.

Ya kara da cewa kwana uku bayan hakan wani dalibi ya kamu da cutar bayan gwajin da akayi masa ranar 6 ga Oktoba.

Abayomi ya tabbatarwa yan jihar Legas cewa gwamnatin na daukan matakan da ya kamata domin shawo kan lamarin.

Ya bayyana cewa an sanar da dukkan iyaye kuma an shawarcesu kan abinda ake ciki a ranar 13 ga Oktoba.

An tattauna da iyayen ne a taron Zoom na yanar gizo.

Daga komawa, malamai da dalibai 181 sun kamu da Korona a makaranta daya a Legas
dalibai
Asali: Getty Images

A wani labari daban, AFP ta ce akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya saba dokar yaki da annobar COVID-19 da dawowansa Italiya da ya yi bayan ya kamu.

Ministan wasanni na Italiya, Mista Vincenzo Spadafora, ya yi magana a ranar Alhamis game da dawowar Ronaldo daga kasar Portugal.

Game da saba doka, da aka tambayi Ministan, sai ya ce: “Eh, ina tunanin haka, idan babu tabbatacciyar izini daga hukumomin lafiya.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel