Guinea Bissau: An saka wa wani layi sunan Buhari saboda ƙimarsa da tsoron Allah

Guinea Bissau: An saka wa wani layi sunan Buhari saboda ƙimarsa da tsoron Allah

- Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Embalo ya saka wa wani layi a Bissau sunan Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

- Shugaba Embalo ya ce ya yi hakan ne don don karramawa da kuma mutunta Shugaba Buhari saboda gaskiyarsa da tsoron Allah

- Shugaban na Guinea Bissau ya kuma jinjinawa Shugaba Buhari saboda goyon baya da tallafi da ya ke bayarwa wurin yaki da 'yan ta'adda a Tafkin Chadi

Shugaba Umaro Embalo ya mika godiyarsa ga Shugaba Buhari bisa goyon baya da shawarwari da ya ke bashi tun kafin rantsar da shi da bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Guinea Bissau.

Shugaban Guinea ya saka wa wani layi sunan Buhari saboda 'tsoron Allansa'
Shugaban Guinea da Shugaba Buhari. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Shugaba Embalo ya yi bayanin cewa ya saka wa wani layi a Bissau, babban birnin jihar sunan Shugaba Buhari don karramawa da kuma mutunta shugaban na Najeriya saboda gaskiyarsa da tsoron Allah.

A bangarensa, Shugaba Macky Sall na Senegal ya yaba yadda Najeriya ke bada gudunmawa wurin yaki da 'yan ta'adda da ake yi a yankin Tafkin Chadi.

Shugaban na Senegal ya yi wannan yabon ne bayan wani liyafar cin abinci bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja a daren ranar Alhamis.

Ya kuma jinjinawa Najeriya bisa goyon bayan da ta ke bawa kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, a yunkurin ta na samar da saman lafiya a Mali.

KU KARANTA: PSC za ta kori tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki

Ga wani bangare cikin jawabin da ya yi, "Abinda zan ce shine ban san cewa tun farko ECOWAS na cikin masu kokarin kawo zaman lafiya a Mali ba. Tabbas Mali na daya daga cikin manyan kasashen ECOWAS

"Kamar yadda kuka sani, 'Yan ta'adda suna barazana ga Mali har ma Jamhuriyar Nijar, ina son jinjinawa kokarin da Najeriya ke yi wurin yaki da Boko Haram da yadda ta ke bada gudunmawar kudi wurin yakin da ake yi a Tafkin Chadi.

"Najeriya kuma tana tallafawa ECOWAS har da Mali, Nijar da Burkinsa Faso inda muke cikin wani mawuyacin hali."

Daga karshe ya yi wa Shugaba Buhari godiya bisa irin tarbar girma da karamci da ya yi musu na gargajiya kana ya mika godiyarsa da jami'an gwamnati da suka hallarci taron.

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta tsare wani ma'aikacin gidan gyaran hali mai suna Danladi Bako bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin tabar wiwi ce.

Mallakar tabar wiwi laifi ne da aka tanadarwa hukunci a sashe na 19 na dokar hukumar NDLEA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel