Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)

Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)

- Hedkwatar tsaron Najeriya DHQ ta alanta nasarar sojin sama a jihar Borno

- A harin da aka kai jiya, Sojin sun hallaka dimbin yan bindigan tare da ragargaza mabuyarsu

- Sojin sun samu labarin kasancewar yan bindigan a wajen ne daga bakin mutane

Rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) karkashin atisayen Operation LAFIYA DOLE sun samu nasarar ragargaza wani sansanin yan ta'addan Boko Haram da ISWAP dake yankin tafkin Chadi a Borno.

Jami'an sun samu nasarar yin hakan ne a harin da suka kai ranar Alhamis, 15 ga Oktoba.

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa "rundunar sojin sun kashe yan ta'addan ISWAP da dama kuma suka ragargaza sansaninsu dake Tudun Wulgo da Tumbin Gini dake yankin tafkin Chadi dake jihar Borno."

A jawabin da kakakin hedkwatar tsaro ya saki a shafinta na Tuwita, ya ce "an samu nasaran hakan ne a ruwan saman da aka kai jiya 15 ga Oktoba, 2020 karkashin hari mai taken "WUTAR TAFKI,."

KU KARANTA: Shugaban 'yan sandan Najeriya ya gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga

Kalli bidiyon harin:

DUBA NAN: Bidiyon jami'in dan sanda rike da bindiga yana nadin tabar wiwi ya bayyana

Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)
Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo) Credit: @DefenceinfoNG
Asali: Twitter

A bangare guda, wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka yi takaddama tsakanin wasu jami'an sojoji da yan sanda a kan titi.

A cikin bidiyon, ana iya ganin lokacin da wani jami'in Soja yake marin dan sanda kan abinda yake yiwa fasinjojin dake wucewa.

Mun ji Sojan yana magana yana dukan dan sandan: "Me yasa kuke amsan kudi a hannunsu, ku mayar musu da kudadensu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel