Sojoji sun suburbudi yan sanda masu amsan na goro hannun mutane a kan titi (Bidiyo)

Sojoji sun suburbudi yan sanda masu amsan na goro hannun mutane a kan titi (Bidiyo)

- - Yayinda gwamnati ke alkawarin gyare-gyare a hukumar yan sanda, wani bidiyo ya bayyana

- An ga bidiyon Sojoji na dukan yan sanda suna umurtansu su mayarwa mutane kudaden da suka karba daga hannunsu

Abubuwan mamaki na faruwa a Najeriya kulli yaumin musamman tsakanin jami'an tsaron Najeriya.

Wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka yi takaddama tsakanin wasu jami'an sojoji da yan sanda a kan titi.

A cikin bidiyon, ana iya ganin lokacin da wani jami'in Soja yake marin dan sanda kan abinda yake yiwa fasinjojin dake wucewa.

Mun ji Sojan yana magana yana dukan dan sandan: "Me yasa kuke amsan kudi a hannunsu, ku mayar musu da kudadensu."

DUBA NAN: Shugaban 'yan sandan Najeriya ya gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga

Kalli bidiyon:

A wani labarin daban, wani fai-fain bidiyon jami'in dan sandan Najeriya ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka gansa yana nadin tabar wiwi a bainar jama'a rike da bindigarsa.

Sojoji sun suburbudi yan sanda masu amsan na goro hannun mutane a kan titi (Bidiyo)
Sojoji sun suburbudi yan sanda masu amsan na goro hannun mutane a kan titi (Bidiyo) Credit: @bakintiti
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamnan Yobe ya yiwa mutumin da ya mayar da kudi N1.7m kyauta mai tsoka

Wannan bidiyon ya bayyana ne lokacin da matasan Najeriya ke zanga-zangan neman sauyi a hukumar yan sandan Najeriya saboda irin cin zarafin da suke yiwa yan Najeriya.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa ire-iren wadannan yan sanda ke kashe matasa bayan sun bugu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel