Hadimai na 120 sun min kaɗan - Shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

Hadimai na 120 sun min kaɗan - Shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

- Alhaji Ɗanlami Idris Odasko, shugaban ƙaramar hukumar Eggon ya jihar Nasarawa ya ce hadimansa 120 sun yi kaɗan

- Shugaban ƙaramar hukumar ya ce idan da yana da hali zai ƙara adadin su zuwa 200 ko 300

- A cewarsa, galibin hadiman matasa ne marasa aikin yi don haka ɗaukan su aiki da ya yi yafi alheri maimakon barinsu suna ɓarna a gari

Hadimai na 120 sun min kaɗan - Shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa: Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

Shugaban ƙaramar hukumar Eggon a jihar Nasarawa, Alhaji Ɗanlami Idris Odasko, ya ce hadimansa 120 sun masa kaɗan.

"Ina da hadimai guda 120.

"Idan ina da ƙarin hanyoyin kuɗin shiga, zan ƙara adadin su zuwa 200 ko 300.

"Mafi yawancin hadiman nawa matasa ne da ke neman abinda za su rike kansu da shi.

"Barin su haka nan kara zube ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba a garuruwan mu," in ji shi.

KU KARANTA: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

Ya ce baya da zaɓaɓɓun ƴan siyasa, hadimai suna da muhimmanci domin su kan taimaka wurin wayar da kan mutane game da tsare-tsaren gwamnati.

Odasko ya ce biyan hadimansa N10,000 zuwa N20,000 ya fi alheri a maimakon kashe kudade masu yawa wurin yin gyara idan an bar su ba aiki suna ɓarna.

A wani labarin daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel