Gwamnan Yobe ya yiwa mutumin da ya mayar da kudi N1.7m kyauta mai tsoka
- Gaskiya ta fi kwabo, gaskiyar wani dattijo ta biya Malam Kiri Umaru da ya mayar makudan kudin da ya tsinta
- A lokuta daban-daban, direban ya tsinci kudi N1.7m kuma ya mayarwa masu shi
- Gwamnan jiharsa ta Yobe, Mai Mala ya aike masa da tukwici mai albarka
Legit.ng ta tattaro cewa gamayyar kungiyoyin yan fafutuka a jihar Yobe watau Network for Yobe Civil Society Organisations (NYCSO) ta baiwa Malam Kiri Umaru lambar yabon jakadan gaskiya da kana'a.
Hakazalika, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya aikewa mutumin da kudi N250,000 da kayan masarufi.
A cewar gwamnan, ya bashi kudin ne domin kara masa karfin gwiwa kuma hakan ya zama darasi ga mutane domin su kwaikwayi irin wannan hali.

Asali: UGC
KU KARANTA: Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno
Mun kawo muku cewa Jaridar Daily Trust ta kawo labarin wani Malam Kiri Umaru, wanda direban mota ne a garin Damatutu, jihar Yobe, da ya maida miliyoyin kudi.
Kiri Umaru ya maida Naira miliyan 1.7 da ya tsinta a mabanbamtan lokuta ga masu kudin.
Wannan mutumi ya shafe shekaru 40 ya na tuka fasinjoji da kayan jama’a a kauyuka da manyan garuruwa, abin da bai yi shi ne gaba da kudin jama’a.
A duk lokacin da Kiri Umaru ya tsinci kudi a cikin motarsa ko a wani wuri, sai ya yi kokari ya maida su wanda ya yi sakaci ko gaggacin zubar da su.
DUBA NAN: FAAC ta rabawa Gwamnatoci Naira Biliyan 639 a matsayin kason Satumba
Jaridar ta ce Umaru mai shekaru 60 a Duniya ya na da mata biyu da ‘ya ‘ya har 12 wanda duka sun dogara da shi ne kafin su iya sa abinci a bakinsu.
Kudin da wannan mutumi ya tsinta karshe su ne N1, 380, 000 na wani da aka kunshe a bakar leda. Umaru ya dauki wannan kudi ya kai wa ‘yan kamasho.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng