'Yar majalisar jihar Ondo da aka kora don zargin zagon kasa ta yi martani

'Yar majalisar jihar Ondo da aka kora don zargin zagon kasa ta yi martani

- Ƴar majalisar jihar Ondo Misis Favour Tomowewo ta ce babu wanda ya kore ta daga jam'iyyar APC

- Ƴar majalisar ta yi wannan martani ne biyo bayan rahotannin da suka bazu cewa an kore ta saboda zargin yiwa jam'iyyar zagon ƙasa

- Tomowewo ta ce kawo yanzu ba ta samu takardar kora daga hannun shugaban mazabar ta ba don haka ta ce ayi watsi da labarin korar tan da ya bazu

Har yanzu ni 'yar APC - 'Yar majalisar Ondo da aka kora
Favour Tomowewo. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

Ƴar majalisar jihar Ondo, Misis Favour Tomowewo ta ce har yanzu tana nan daram a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, inda ta ce babu wanda ya kore ta daga jam'iyyar.

An sanar da cewa an kore Tomowewo wacce ke wakiltar mazabar Ilaje 2 a majalisar jihar daga jam'iyyar kan zargin ta da yi wa jam'iyyar zagon kasa a zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar a jihar.

KU KARANTA: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

Wasikar korar ta na ɗauke da sa hannun Shugaban jam'iyyar gundumar Mahin, Mista Olagoke Ajimuda da sakataren Mista Omosule Taid.

Sai dai, Tomowewo cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta ce bata samu wasikar kora ba daga shugaban mazabar ta inda ta ce rahoton korar ta ƙarya ne.

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Ma'aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel