Duk laifinku ne, daliban jami'a ne suka cika wuraren zanga-zanga - Minista ya daura laifi kan ASUU

Duk laifinku ne, daliban jami'a ne suka cika wuraren zanga-zanga - Minista ya daura laifi kan ASUU

- Ministan kwadago ya bayyana dalilin da yasa zanga-zangan ENDSARS ta ki karewa

- Bayan watanni bakwai da yajin aiki, gwamnati ta gayyaci ASUU zama a teburin sulhu

- ASUU ta lashi takobin cewa mambobinta ba zasuyi rijista a manhajar IPPIS ba

Gwamnatin tarayya ta koka cewa daliban jami'o'in Najeriya da ya kamata ace sun koma makaranta ne aka dauka suna zanga-zangan #EndSARS a fadin tarayya.

Ta daura laifin kan yajin aikin da kungiyar Malaman jami'a ASUU suke yi.

Minitan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana hakan ne a zaman sulhun da ya jagoranta tsakanin gwamnati da jami'an ASUU ranar Alhamis a Abuja.

A cewar kamfanin dillancin labarai a Najeriya NAN, Ngige yace, "Tsawon mako daya yanzu, hankulanmu sun tashi, muna ta ganawa kuma muna addu'a zamanmu ya haifar da 'da mai ido."

"Ba dadi muke ji ba muna ganin yaranmu da ya kamata ace suna makaranta ana amfani da su wajen zanga-zangan #EndSARS, #EndStrike, #EndSWAT."

"Zamu yi iyakan kokari wajen ganin cewa mun hadu a tsakiya saboda mu magance wannan rikici domin amfanin kasa ga baki daya."

KU KARANTA: Ganduje ya amince da fitar da N2.3bn don zaben kananan hukumomi a Kano

Duk laifinku ne, daliban jami'a ne suka cika wuraren zanga-zanga - Minista ya daura laifi kan ASUU
Ganawa Hoto: Ofishin ministan kwadago
Asali: Twitter

Ministan yace gwamnatin tarayya ta fara gwajin manhajar biyan albashin UTAS da malaman jami'o'in suka kera.

Ya ce mambobin ASUU sun yi ikirarin cewa manhajar ta game dukkan abubuwan ake yi a jami'o'i kuma za a yi gwaje-gwaje sau uku cikin lokacin da kungiyar ta baiwa gwamnati.

DUBA NAN: Hukumar Hizbah ta lalata kwalaben giya 883 a jihar Bauchi

"Muna da rahotannin fari da gwaji kan UTAS, kuma muna kyautata zaton cewa za muyi abinda ya dace."

"Bari in bayyanawa yan jaridar, bamu ce UTAS za ta maye gurbin IPPIS ba, kamar yadda wasu rahoton." Yace.

A bangare guda, majalisar zartarwa ta yi na’am da kashe Naira biliyan 1.28 domin sayen na’urorin tsaro da za a kafa a tashoshin jirgin kasan Abuja-Kaduna-Kano.

Hukumar NAN ta ce gwamnatin tarayya ta cin ma wannan matsaya ne a taron mako-mako na FEC wanda aka yi a ranar Larabar nan, 14 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel