Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno

Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno

- Gwwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kai wa jama'ar Jere tallafi

- Ya bai wa iyalai 5,000 kayan abinci a cikin karamar hukumar Jere ta jihar Borno

- Daga nan ya zarce zuwa sansanin zakakuran sojin Najeriya inda ya kara musu karfin guiwa

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Alhamis ya ziyarci karamar hukumar Jere inda ya raba kayan abinci ga iyalai 5,000 mabukata, ya duba yadda wasu ayyuka uku suke tafiya da kuma karfafa wa sojoji guiwa.

Zulum ya kai ziyara zuwa Gongulong Lawanti, Khaddamari da Zabarmari duk a cikin karamar hukumar Jere.

A Gongulong Lawanti, gwamnan ya raba kayan abinci ga iyalai 4,000 yayin da wasu iyalan 1,000 suka amfana da tallafin a Khaddamari. Zulum ya ziyarci Zabarmari.

A dukkan yankuna, gwamnan ya samu ganawa da jama'ar. Ya bada umarnin hanzarta karasa ayyukan titin Zabarmari zuwa Maiduguri, gina cibiyar lafiya da kuma gina wata makaranta.

Zulum ya bada umarnin karasa ginin cibiyar lafiya da ke Gongulong wacce aka fara lokacin mulkin Gwamna Kashim Shettima.

Yayin da yake Jere, gwamnan ya ziyarci rundunar ta 195 da ke Zabarmari, Khaddamari da Gongulong Lawanti domin kara musu karfin guiwa.

A yayin da yake jawabi yayin ziyarar, ya ce, "A madadin gwamnatina da dukkan jama'ar jihar Borno, ina mika godiyarmu gareku.

"Ya zama dole in jinjina muku. Duk mun san sadaukarwar da kuke yi, wasu daga cikinku baku ganin iyalanku na tsawon lokaci duk domin ku bai wa rayukanmu da dukiyoyinmu kariya. Mun gode," Zulum ya sanar da zakakuran sojojin.

KU KARANTA: EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo

Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno
Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon budurwa ta tsayar da jirgin sama sannan ta sauka saboda ba za ta iya ajiye jakarta mai tsada ba a kasa

A wani labari na daban, wasu daga cikin gwamnonin arewa, suna jin dadin ayyukan da SARS keyi kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya bayyana.

Gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya bayyana ra'ayin gwamnonin arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sanar da manema labaran gidan gwamnatin hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel