Ganduje ya amince da fitar da N2.3bn don zaben kananan hukumomi a Kano

Ganduje ya amince da fitar da N2.3bn don zaben kananan hukumomi a Kano

- Majalisar zartaswar jihar Kano ta yi zamanta a ranar Laraba kamar yadda ta saba

- Majalisar ta amince da sakin wasu kudade a ayyuka domin alfanun mutan jihar

- Wa'adin shugabannin kananan hukumomi da kansilolin kananan hukumomin jihar 44 na gab da karewa

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da N2.3 billion domin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar da aka shirya yi ranar 16 ga watan Junairu, 2021.

Kwamishanan labaran jihar, Muhammad Garba, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Kano.

Za ku tuna cewa hukumar gudanar da zaben jihar Kano KANSIEC ta zabi ranar 16 ga Junairu domin zabe shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da kansiloli 484 saboda wa'adin wadanda ke kai yana gaba da karewa.

An yi zaben kananan hukumomin a karshe Febrairun 2018.

Garba ya ce an amince da fitar da kudin ne a zaman majalisar zartarswar jihar da akayi ranar Laraba a gidan gwamnatin Kano.

Yace: "Bayan sakin bayanai yadda za'a gudanar da zaben 16 ga Junairu na kananan hukumomi, an bada izinin fitar da kudin domin sayen kayayyakin aiki na kudi N2.3 billion."

Ganduje ya amince da fitar da N2.3bn don zaben kananan hukumomi a Kano
Hoto: @dawisu Ganduje
Asali: UGC

DUBA NAN: Hukumar Hizbah a Bauchi ta lalata kwalaben giya 883 a jihar Bauchi

A bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa da Rimin Gado, Tijjani Jobe, da ya dakata da wani aikin titi da ya fara a mazabarsa.

Babban tiitin Rimingado zuwa Gulu ya kasance cikin wani mawuyacin hali sama da shekaru 30, duk da kuwa amfaninsa ga jama'ar Gulu masu noman dankali da sauran mazauna yankin.

Tun farko dai dan majalisar ne ya mika bukatar aiki ga ma'aikatar noma ta tarayya a matsayin tallafin korona ga yankunan karkara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel