NYSC: Za a yi wa masu bautar kasa gwajin COVID 19 - FG

NYSC: Za a yi wa masu bautar kasa gwajin COVID 19 - FG

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a yi wa masu bautar ƙasa hidima da ma'aikatan sansanin NYSC gwajin Korona kafin bude sansanonin

- Gwamnatin ta sanar da hakan ne ta bakin Sani Aliyu, shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona

- Aliyu ya ce za a yi wa kowa gwajin cutar Korona kafin fara bada horo da wayar da kai a sansanonin da ke fadin Najeriya

DUBA WANNAN: An damƙe wanda ya maye gurbin Gana

Bude sansanin 'yan NYSC: Za a yi wa masu yi wa kasa hidima gwajin COVID 19 - FG
Masu yi wa kasa hidima, NYSC. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya ta ce za a yi wa dukkan wadanda za su shiga sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) gwajin cutar COVID 19 gabanin buɗe sansanonin a fadin kasar.

Ta kuma ce za a bude sansanonin bada horon na ƴan NYSC a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Sani Aliyu ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi a Abuja.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

An rufe sansanonin bawa ƴan yi wa ƙasa hidimar horo tun a watan Maris na 2020 don daƙile yaɗuwar cutar Korona.

Amma da ya ke magana a ranar Alhamis, Aliyu ya ce, "Mun tanadi matakai tare da NCDC (Hukumar Ƴaki da Cututtuka Masu Yaɗuwa) da NYSC wurin shirin buɗe sansanonin a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020.

"PTF ɗin kuma ta tanadi ƙarin matakan kariya da suka haɗa da yi wa masu yi wa ƙasa hidima da ma'aikatan sansanin gwajin COVID 19 kafin fara bada horon."

Tunda farko, kun ji cewa, gwamnatin tarayyar ta amince da bude dukkan sansanonin horas da masu yi wa kasa hidima ta NYSC a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020.

Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya rubuta, "An amince da bude sansanonin horas da wadanda za su yi wa kasa hidima a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020. Za a samar da matakin dakile yaduwar Covid 19."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel