Hukumar Hizbah ta lalata kwalaben giya 883 a jihar Bauchi

Hukumar Hizbah ta lalata kwalaben giya 883 a jihar Bauchi

- Kamar yadda akeyi a Kano da Jigawa, hukumar Hisbah ta damke masu sayar da kayan maye

- Hisbah ta lalata kwalaben giya sama da 800 a harin da ta kai kwanakin baya

- Kwamandan hukumar na Bauchi ya lashi takobin gurfanar da wadanda aka kama a kotu

A cikin matakan da take dauka domin tabbatar da bin Shari'ar Musulunci a jihar Bauchi, hukumar dabbaka Shari'a watau HIzbah ta fasa kwalaben barasa da kayen maye 883.

Kwamandan Hizbah, Ibrahim Yisin, ya ce an kwace wasu kayen maye a sassan cikin gari a wuraren banbadewa, otal-otal da wuraren da ake sayar da su, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamanda Yisin ya ce za'a gurfanar da wadanda aka kama a kotu.

"Lalata kwalaben giya ya biyo bayan umurnin da hukumar ta baiwa masu sayarwa cewa su daina."

"Zamu cigaba da kokari wajen sintiri kulli yaumin domin kare al'ummarmu."

"Shari'ar Musulunci a jihar Bauchi ta amince da sayar da kayan maye da sha a wasu zababbun wurare irinsu barikin sojoji, barikin yan sanda da gidajen shakatawa," Yace.

Ya tabbatar da cewa hukumar zata hukunta wadanda suka saba dokar PenalCode na Cap 108, sashe na 403(1-2).

KU KARANTA: An haramta zanga-zanga a birnin tarayya Abuja

Hukumar Hizbah a Bauchi ta lalata kwalaben giya 883 a jihar Bauchi
Hukumar Hizbah Hoto: Hisbah a Kano
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ban yi laifi ba don na yi takara, burin kowa shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli

A baya mun kawo muku rahoton cewa hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta damke wasu matasa biyu da ake zargi da laifin Luwadi a karamar hukumar Dutse.

Kwamandan hukumar Hisban jihar, Malam Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan yayinda yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ranar Laraba.

Ya ce an damke matasan biyu. masu shekaru 32 da 20, a wani dakin Otal dake Dutse, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa wasu makwabta suka kawo musu kara yayinda suka ji hayaniyansu suna rikici kan kudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel