Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

- Malam Fulani Kwajafa ya nuna alhininsa akanrundunar 'yan sanda ta SARS din da aka rusa

- Tsohon dan sandan yace an kirkira rundunar ne don yaki da fashi da makami a fadin kasar nan

- Jaridar Legit.ng ta gane cewa yana daya daga cikin 'yan sandan da suka kirkiri SARS a mulkin Buhari na soji a 1984

Fulani Kwajafa, tsohon dan sanda ne wanda ya jagoranci kirkirar SARS, ya nuna danasaninsa na kirkirar rundunar a hirarsa da BBC Hausa a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba.

Ana tsaka da zanga-zangar rushe rundunar, Kwajafa yace an kirkire su ne don yaki da fashi da makamai a fadin Najeriya.

Kwajafa ya sanar da yadda aka kirkiri SARS a shekarar 1984, lokacin Etim Inyang ne sifeto janar na 'yan sanda lokacin Buhari na Shugaban kasa na mulkin soji.

"Amma sai dai daga labaran kungiyar da nake ji, sun canja salon aikin nasu, duk sai naji takaici da danasanin kirkirar kungiyar," yace.

Tun daga ranar Alhamis din makon da ya gabata ne matasa a yankin kudancin kasar nan da babban birnin tarayya suke zanga-zanga.

Suna yin hakan ne domin neman a rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makamai a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Ganduje ya saka hannu a kan sabuwar dokar masarautu ta Kano

Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama
Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama. Hoto daga Premiumtimes.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon El-Rufai ya durkusa a gaban Sarki Ahmad Bamalli ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Alhamis ya bayyana ranar zaben shugaban kasa mai zuwa.

Ya bayyana cewa, za a yi zaben a ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 idan akwai rai, lafiya da zaman lafiya kamar yadda the Nation ta wallafa.

A sakon fatan alherinsa a yayin rantsar da kwamitin wucin-gadi na musamman a kan sake duba kundin tsarin mulkun kasar nan, shugaban hukumar zaben ya sanar da 'yan majalisar wakilai cewa akwai kwanaki 855 da suka rage kafin zaben.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel