EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo

EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, yace a shirye gwamnatin tarayya take wurin tallafawa matasa

- Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inda yace gwamnati na iya kokarinta akan matasa

- Ya kara da cewa, ya kamata matasa su lura da yadda gwamnati ke hanzarta gyara a duk wani al'amarin da suka yi korafi akanshi

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, yace hankalin gwamnatin tarayya na wurin matasan Najeriya.

A wata hira da manema labarai suka yi dashi a ranar Alhamis a Abuja, Osinbajo yace, gwamnatin Buhari ta mayar da hankalinta akan duk wani abu da zai taimaki matasa su samu ayyukan yi da bunkasa sana'o'insu.

Don haka ne yace, yakamata matasa su yi amanna da gwamnati, su san cewa a shirye take da ta tallafa musu a koyaushe.

A cewarsa, abinda matasa ya kamata su sani shine, gwamnatin tarayya ta mayar da dukkan hankalinta akansu.

"Muna da niyyar yin iyakar kokarinmu don amfani da abubuwan da muke da su a hannu. Yakamata matasa su fahimci cewa, muna gaggawar yin duk wani gyara akan wata barakar da suka yi korafi," yace.

KU KARANTA: IGP ya kaddamar da sabuwar makarantar 'ya'yan 'yan sanda a Daura

EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo
EndSWAT: FG tana tunanin matasa, damuwarku tana damunmu - Osinbajo. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

A wani labari na daban, majalisar zartarwa ta tarayya wadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta ta amince da karin Naira Biliyan 8 don tagwaita titin Kano zuwa Maiduguri wanda ya ratsa ta Wudil.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya sanar da hakan bayan taron sati da aka yi ranar Laraba, inda yace an kiyasta kashe naira biliyan 63 don aikin titin Kano zuwa Maiduguri wanda ya mike dodar na tsawon Kilomita 560.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel