Yanzu-yanzu: An haramta zanga-zanga a birnin tarayya Abuja

Yanzu-yanzu: An haramta zanga-zanga a birnin tarayya Abuja

- Kamar Rivers, an haramta zanga-zangar #ENDSARS a birnin tarayya Abuja

- Ministan Abuja, Musa Bello, ya ce an yi hakan ne don kare rayukan mutane daga cutar Korona

- Ana kan sanarwan matasa suka garzaya majalisar dokokin tarayya suna zanga-zanga

Ministan birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya haramta zanga-zanga a birnin kuma ya yi hakan ne saboda matasan dake rajin kawo karshen zalunci da zarafin da yan sanda ke yiwa yan Najeriya wanda aka yiwa take #ENDSARS.

A jawabin da hukumar birnin tarayya FCTA ta saki, kwamitin tabbatar da tsaron Abuja ta haramta zanga-zanga inda tayi zargin masu yi da sabawa dokokin COVID-19.

DUBA NAN: Allah ya yiwa jagoran Musulma a yankin Igbo, Sheik Adam Akachukwu Idoko, rasuwa

Jawabin da sakataren yada labaran ministan, Mr Anthony Ogunleye, ya rattafa hannu, yace "duk da cewa kwamitin tana sane da hakkin yan Najeriya na zuwa inda suka ga dama kamar yadda kundin tsari mulki ta tanada, an lura cewa yadda aka taron tururuwa yayin zanga-zanag ya sabawa sharrudan kariya daga COVID-19."

A cewan ministan, "wannan sabawa doka da ake yi na da hadari ga masu zanga-zangar da sauran jama'an gari."

Saboda haka yace "kwamitin ta bada umurnin haramta dukkan zanga-zanga, yawon titi a cikin birnin tarayya saboda hadarin kamuwa da COVID-19."

Yanzu-yanzu: An haramta zanga-zanga a birnin tarayya Abuja
Kwamitin tsaro Credit: @OfficialFCTA
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ban yi laifi ba don na yi takara, burin kowa shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli

A wani labarin, ministan gwamnatin tarayya, Festus Keyamo SAN, ya koka game da zanga-zangar #EndSARS da ake cigaba da yi a fadin jihohin kasar nan.

Festus Keyamo ya bayyana cewa a sanadiyyar zanga-zangar da wasu su ke ta yi da nufin rusa jami’an SARS ne ya rasa mai tuka masa mota.

Ministan ya bada labarin yadda direbansa ya mutu wajen zanga-zangar. Ya ce masu zanga-zanga su ka zama ajalin Yohanna Shankuk a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel