Da duminsa: Allah ya yiwa jagoran Musulma a yankin Igbo, Sheik Adam Akachukwu Idoko, rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa jagoran Musulma a yankin Igbo, Sheik Adam Akachukwu Idoko, rasuwa

- Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!

- Sheikh Adam Idoko ya kasance babban jagora ga Musulman kasar Igbo

- Hukumar jin dadin alhazan Najeriya ta bayyana jimaminta bisa rashin shugaban yankinta na Enugu

Rahoton da ke shigo mana na nuna cewa Allah ya yiwa mataimakin shugaban al'ummar Musulman jihar Enugu, Sheik Adam Idoko, rasuwa.

Majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta sanar da hakan da safiya Alhamis, 15 ga Oktoba 2020.

Shugaban sashen yada labarai na NSCIA, Aselemi Ibrahim, ya bayyana alhinin majalisar bisa mutuwar Sheikh Adam.

Ya bayyana cewa babban limanin ya rasu ne a birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020 a asibitin kasa.

"Shugabancin majalisar koli ta shari'ar Musulunci NSCIA tana mai sanar da rasuwar mataimakin majalisar lamuran Musulunci a jihar Enugu, Sheikh Adam Akachukwu Idoko rasuwa ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2020 a asibitin kasa dake Abuja," yace.

"Kawo lokacin mutuwarsa, Sheik ahmad Idoko, ya kasance Sakataren hukumar jin dadin alhazan jihar Enugu kuma babban Limamin Jami'ar Najeriya dake Nsukka (UNN)."

"Ya rasu ya bayar mata daya da yara 3. Muna addu'a Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya azurtashi da Jannatul Firdaus."

Da duminsa: Allah ya yiwa jagoran Musulma a yankin Igbo, Sheik Adam Akachukwu Idoko, rasuwa
Sheik Adam Akachukwu Idoko, rasuwa Credit: @nigeriahajjcom
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ban yi laifi ba don na yi takara, burin kowa shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli

A bangare guda, MURIC ta yi magana a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020, ta na kiran a dakatar da zanga-zangar #EndSARS da ake yi a bangarorin kasar nan.

MURIC mai wayar da kan jama’a game da hakkokin musulmai, ta gargadi masu wannan zanga-zanga da cewa su yi hattara da mugun nufin wasu.

Kungiyar ta ja-kunnen wadanda ke wannan zanga-zanga da cewa su bi sannu ka da ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen cin ma manufarsu ta boye.

DUBA NAN: Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel