Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure

Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure

- Matasa 12 sun hadu a shirin NYSC na yiwa kasa hidima na tsawon shekara daya, inda suka yi soyayya tare da auren juna a jihar Anambra

- Hukumar NYSC reshen jihar suka yanke shawarar hada liyafa don taya ma'auratan murna

- An dora hotunan ma'auratan a shafukan sada zumunta, inda har aka ga wasu daga cikin ma'auratan suna jiran isowar jariran su

Hukumar da ke kula da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC a jihar Anambra ta hada liyafar taya matasa 12 murnar yin aure a yayin bautar kasarsu ta shekara daya a jihar.

Ma'auratan da suka hadu a rukunin C na masu yiwa kasa hidimar na shekarar 2019, sun hada da Henry Nwachoko, Charles Ruth, Oluchukwu Davis, da Ohale Nkemakolam.

Nsofor Obianuju, Ogberie Collins, Nwokearu Chinyeremaka, Bernard Faith Amarachi, da Okafor Chukwudi, duk sun hadu ne a lokacin da suka je yiwa kasa hidima.

KARANTA WANNAN: #EndSARS: Aisha Yesufu ta aike da muhimmin sako ga matasan Nigeria

Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure
Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure - Facebook/@NYSC Anambra State
Asali: Facebook

A cewar shafin Facebook na hukumar NYSC jihar Anambra, matasan sun yi aure, inda har wasu matan ke dauke da juna biyu.

An taya ma'auratan murna ta hanyar ba su kyaututtuka gami da kudade.

Taron liyafar taya su murnar ya faru ne a babban birnin jihar, kuma ya samu halartar kodinetan shirin na jihar, Mr Kehinde Aremu da mataimakiyarsa, shiyyar Kudu maso Gabas Mrs Ify Nwafor.

KARANTA WANNAN: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Nwafor ta bayyana cewa mutane na shiga shirin NYSC saboda manufofi daban daban, kuma daya daga cikin manufofin shine haduwa da masoya har su yi rayuwa tare.

Wasu daga cikin ma'auratan sun bayyana cewa sun hadu a wurare daban daban kamar addu'ar safe a sansanin horas da matasan da ke Onitsa, da sauransu.

Kalli kyawawan hotunan a kasa:

Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure
Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure - Facebook/@NYSC Anambra State
Asali: Facebook

A wani labarin, wani kwararren likitan idanu a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Dr. Ibrahim Yuguda, ya gargadi 'yan Nigeria da su daina amfani da fitsari da kashin shanu wajen magance ciwon idanu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a bukin 'ranar gani' ta duniya a Kano, Yuguda ya ce babban kuskure ne amfani da sukari, gishiri, ruwa, fitsari ko kashin shanu don maganin ciwon idanu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel