Da duminsa: FG ta sanar da ranar bude sansanonin horas da 'yan NYSC

Da duminsa: FG ta sanar da ranar bude sansanonin horas da 'yan NYSC

- Gwamnatin tarayya ta bada umurnin a bude sansanonin bawa masu yi wa kasa hidima horo a ranar 10 ga watan Nuwamba

- Sanarwar ta fito ne daga bakin Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare cikin wani sako da ya wallafa a Twitter a ranar Alhamis

- Ministan Matasan ya ce gwamnati za ta tanadi matakan dakile yaduwar cutar korona a sansanonin bawa masu yi wa kasa hidimar horo

Da duminsa: FG ta sanar da ranar bude sansanonin horas da 'yan NYSC
'Yan NYSC a Najeriya. Hoto daga @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da bude dukkan sansanonin horas da masu yi wa kasa hidima ta NYSC a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020.

Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya rubuta, "An amince da bude sansanonin horas da wadanda za su yi wa kasa hidima a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020. Za a samar da matakin dakile yaduwar Covid 19."

DUBA WANNAN: An bayyana ranar buɗe makarantun gaba da sakandare a jihar Kano

A ranar 18 ga watan Maris ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada umurnin rufe dukkan sansanonin horas da masu yi wa kasa hidiman don fargabar yaduwar annobar korona.

A wani labarin daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Gwamnan da yace malamai su koma aiki ranar 1 ga watan Nuwamba ya kara da cewa za a bada umurnin ɗaukan sabbin malamai nan take bayan kammala aikin tantance su da ake a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel