Ban yi laifi ba don na yi takara, burin kowa shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli

Ban yi laifi ba don na yi takara, burin kowa shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli

- Sarkin Zazzau ya kai ziyararsa ta farko gidan gwamnatin Kaduna bayan zabensa sabon sarki

- Ahmed Bamalli ya ce yana kokarin hada kan dukkan wadanda sukayi takara tare

- Ya godewa gwamnan jihar bisa zabensa da yayi cikin sauran

Sabon sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce buri da alfaharin ko wani dan gidan sarauta shine ya zama sarki wata rana.

Ambasada Bamalli ya bayyana hakan ne yayinda ya kaiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, a gidan Sir Kashim Ibrahim.

Sarkin wanda yace takara irin wannan abune dake faruwa a ko ina yace "ko shakka babu mutane zasu nemi hawa kujera duk lokacin da aka samu gurbi, da sharadin cewa yan gidan sarauta ne."

"Ba laifi bane, kuma ina jadaddawa, ba laifi bane, wani mai son mulki ya nemi kujerar Sarki. Amma bayan takaran, ya zama wajibi mu hada kai domin yiwa al'umma aiki,"

"Kuma burin ko wani dan gidan sarauta shine wata rana ya zama sarki." yace.

Sarki Bamalli ya bayyanawa El-Rufa'i cewa yana tuntubar dukkan wadanda sukayi takara domin ciyar da masarautar gaba.

"A makon daya gabata, na samu hadin kai daga wajen kwamitin masu zaben sarki, yan majalisan sarki, dakatai da al'ummar Zariya fiye da yadda nike tsammani." Ya kara.

KU KARANTA: Tarar N10bn: Na shirya yafewa Adams Oshiomole - Gwamna Samuel Ortom

Burin kowani dan gidan sarauta shine ya zama Sarki - Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli
Ahmad Bamalli
Asali: Original

KU KARANTA: Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834

LEGIT Hausa ta kawo muku cewa gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, da ya zama adali ga dukkanin al’umman masarautar.

Gwamnan ya fada ma sarkin cewa gasar neman kujerar ya kare don haka akwai bukatar sarkin ya hada kan mutane, harda wadanda basu goya masa baya ba.

Gwamna El-Rufai ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar sarkin a gidan gwamnati yayinda suka kai masa ziyarar godiya a ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel