Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa

Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa

- Dogo Gide, shugaban 'yan ta'addan jihar Zamfara ya ce idan gwamnati na bukatar kwanciyar hankali a jihar, ta hana sojojin sama kai musu hari a maboyarsu

- Yace ya ki amsa gayyatar gwamnatin jihar Zamfara ne, saboda zarginsa da gwamnati da 'yan jarida ke yi na zama dan Boko Haram

- Ya ce yana da damar dakatar da duk wasu hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa jihohin Arewacin Najeriya, cikin kankanin lokaci

Dogo Gide, shugaban 'yan ta'adda dake jihar Zamfara, Arewa maso yammacin Najeriya, yace za su cigaba da kai hari matukar sojojin sama sun cigaba da ragargazar maboyarsu.

A watan Ogusta, rundunar sojin sama ta kaiwa 'yan ta'addan jihar Zamfara da kuma makwabtan jihar Katsina hari, inda suka ragargaza maboyar 'yan ta'addan.

Gide ya musanta zarginsa da ake yi na zama dan Boko Haram, yace kishiyoyin juna ne su.

Jaridar HumAngle ta ruwaito yadda Gide ya hada kai da wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Ansaru, wacce take a Arewa maso gabas a Najeriya.

A wata murya da HumAngle ta samu, Gide yace zargin da gwamnati da gidajen jarida ke masa akan hada kai da wasu 'yan ta'adda ba gaskiya bane.

"Babu wasu 'yan ta'addan da suka fi karfina ( yana nufin dajin Kuyanbana wanda ya hadu da jihar Kaduna, Katsina, Niger da Zamfara) kawai saboda suna takama da makamai," Gide ya fadi cikin nuna isa.

"Idan kunaso ku yaki mutum, to ku same shi har gida, kuma nasan Ubangiji ba zai baku nasara a kaina ba."

Yayi bayanin kin amsa gayyatar da gwamnatin jihar Zamfara tayi masa, saboda zarginsa da hada kai da 'yan Boko Haram da take yi.

Gide yace ya bar duk wani dan ta'adda yana cin karensa babu babbaka saboda su raba hankalin gwamnati.

Ya kara da cewa, "A shirye nake da dakatar da duk wani ta'addanci da kungiyarsa da ta wasu jihohi suke yi, matsawar gwamnati za ta hana sojojin sama kai mana hari musamman a dajin Kuyanbana dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

"Idan gwamnati tana son kwanciyar hankalin al'umma, Inaso a daina kawo mana hari na tsawon wata 1, ni kuma nayi alkawarin hana duk wani ta'addancin a jihar," inji Gide.

KU KARANTA: Hotunan ganawar Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai a Kaduna

Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa
Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so

A wani labari na daban, wasu 'yan daba dauke da makamai sun kai wa 'yan Najeriyan dake zanga-zanga akan zaluncin da 'yan sanda ke yi a Abuja hari.

'Yan daban dake dauke da adduna sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a daidai Berger, bayan kusan awa daya da fara zanga-zangar.

Sun ci mutuncin masu zanga-zangar har da masu wucewa, inda suka lalata ababen hawan dake wurin. Sun lalata akalla motoci 5 take anan, sannan sun ji wa masu zanga-zangar munanan raunuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel