A shirye muke wurin bai wa damokaradiyyar kasar nan kariya - Rundunar soji
- Rundunar sojin Najeriya a shirye take da kare Najeriya daga duk wata tarzoma da kuma tashin hankali da ke tunkarar kasar cewar Sagir Musa
- Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, da kyar wani mai daukan hoto ya guje wa harbin sojoji lokacin da yake daukar bidiyon masu zanga-zanga a majalisar dattawa
- Kamar yadda takardar da ya wallafa ta nuna, rundunar soji na iyakar kokarinta wurin kare Najeriya da damokaradiyya
Rundunar Sojin Najeriya tace a shirye take ta kare Najeriya da damokaradiyyarta komai rintsi.
A wata takardar ranar Laraba, Sagir Musa, mukaddashin kakakin rundunar sojin Najeriya ya ja kunnen masu tada tarzoma da su kiyaye yin duk wani abu da zai cutar da kasar nan.
A ranar Talata ne wani bidiyon wasu sojoji dake cin zarafin wani mai daukar hoton gidan talabijin din ARISE, har da kwace masa kayan aiki a lokacin da yake daukar Bidiyon masu zanga-zanga a majalisar dattawa yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.
Jaridar The Cable ta wallafa yadda ya samu ya guje wa harbin sojoji da kyar.
A wata takarda da aka rubuta washe garin da al'amarin ya faru, Musa yace sojojin Najeriya na iyakar kokarinsu wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Yace, "Rundunar soji na matukar kokarin tankwara farar hula wurin bin dokokin kasa ko yaushe. Don haka an umarci sojoji da su tsaya tsayin-daka wurin dakatar da duk wani mai tada hankulan jama'a."
KU KARANTA: EndSARS: Hotunan mata 6 'yan gwagwarmaya da suka dauka hankali

Asali: Twitter
KU KARANTA: EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so
A wani labari na daban, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Aliyu Atiku Abubakar, ya yi wallafar da ta janyo cece-kuce a shafinsa na Twitter.
Wallafar kuwa ya yi ta ne a kan wannan zanga-zanga ta kawo karshen SARS wacce ta ki ci balle cinyewa.
A wallafarsa, "Juyin juya hali ne ke gabatowa a gagarumar kasar nan da ta fi kowacce kasa yawan mutane a Afrika. Wannan zanga-zanga ta EndSARS ta wuce kawo gyara ga ayyukan 'yan sanda."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng