An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

- Nan ba da daɗewa ba za a wajabta wa dukkan yan Najeriya mallakar lambar shaiɗan zama ɗan kasa wato NIN

- Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dakta Isa Pantami ne ya bayyana hakan yayin da jam'ian NIMC suka ziyarce shi

- Ministan ya ce mallakar lambar na da matuƙar muhimmanci ga duk wanda ke son amfana da ayyukan gwamnati da tallafi

An kusa tilasta wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Pantami
Ministan Sadarwa, Isa Pantami. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Isa Pantami ya sanar da cewa nan gaba za a wajabta wa ƴan Najeriya mallakar lambar shaidar ɗan ƙasa NIN.

Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke karbar baƙuncin tawagar hukumar samar da lambar ɗan ƙasa (NIMC) a ofishinsa da ke Abuja.

Ya kuma bukaci hukumar ta ƙara adadin mutanen da ta ke yi wa rajista duk wata daga 500,000 zuwa miliyan 2.5.

Har wa yau, Pantami ya umurci hukumar ta kafa cibiyoyin sauraron ƙorafin mutane a sassan kasar don warware matsalolin mutane.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

A cikin sanarwar da kakakin ministan Uwa Suleiman ta fitar an gano Pantami ya ce, "ya mayar da hankali don ganin ƴan Najeriya sun samu lambar shaiɗan zama yan kasa" kuma ya yi kira gare su suyi rajista ba tare da bata lokaci ba."

Ya ce;

"Wannan na da muhimmanci don nan gaba mallakar lambar NIN zai zama wajibi don amfana da ayyukan gwamnati da tallafi.

"Shaidar zama ɗan ƙasa ta zamani wajibi ga duk wata ƙasa mai son cigaba kuma ɗaya daga cikin ginshikin tsarin ɗoka."

A wani rahoton daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel