Dan shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da korona - Melania Trump

Dan shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da korona - Melania Trump

- Barron Trump, ɗan shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da Covid 19 da aka fi sani da korona

- Mai ɗakin shugaba Trump, Melania Trump ce ta sanar da haka cikin wani jawabi da ta yi a ranar Laraba

- Amma ta ƙara da cewa Baron mai shekaru 14 ya warke daga cutar inda ta bayyana shi a matsayin matashi mai kuzari

Ɗan shugabanAmurka Donald Trump mai shekaru 14 Barron ya kamu da korona amma bai nuna alamu da bayan iyayensa biyu sun kamu, a cewar mai ɗakin Trump, Melania Trump Kamar yadda Reuters ta ruwaito.

"An yi sa'a yaro ne mai kuzari bai nuna wasu alamu ba," in ji Melania Trump cikin wata jawabi. Ta ce tuni Barron ya warke.

Baron, ɗan shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da korona - Melania Trump
Shugaban Amurka Donald Trump. Hoto daga Saul Loeb/AFP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An damƙe wanda ya maye gurbin Gana

Shugaban na Amurka ya shafe kwanaki uku a asibitin sojoji na Walter Reed bayan sanar da kamuwarsa.

Amma a halin yanzu an sallame shi ya koma gida kana ya sha nanata cewa ya samu sauƙi sosai sakamakon magungunan da aka bashi duk dai bai fayyace ko ya warke ba.

Wasu ƙasashen Turai sun fara dawo da dokar kulle bayan annobar ta fara dawowa gadan-gadan.

Faransa ta saka dokar hana fita yayin da wasu ƙasashen suka fara rufe makarantu suna ɗaukan ɗalibai aiki a fanin lafiya sakamakon dawowan cutar a lokacin yanayin sanyi ke ƙaratawo a cewar Reuters.

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sanar da dokar hana fita da daddare na sati huɗu a Paris da wasu manyan birane sakamakon samun yaɗuwar cutar.

Shima Fafaroma Francis ya ɗauki matakin kare kansa na nisantar masoyansa a jawabinsa da ya saba yi duk mako a ranar Laraba.

Ya nemi afuwar al'umma bisa wannan sabon matakin da ya zama tilas ya ɗauka don kare yaɗuwar annobar.

A wani labarin, Gwamnatin Kano ta tsayar da ranar 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta buɗe makarantun gaba da sakandare bayan watanni bakwai suna rufe.

Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu a jihar, Dakta Mariya Bunkure ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel