Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834

Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834

- Kamar yadda ta saba, hukumar NCDC ta saki adadin yan Najeriya da suka kamu da cutar Korona

- Yayinda ake smaun raguwar masu kamuwa a Najeriya, abubuwa na munana a kasar Ingila

- Har yanzu kasar Rasha kadai ce ta sanar samun rigakafin cutar har guda biyu

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar COVID-19 ta sake harbin sabbin mutane 179 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:15 na daren ranar Laraba 14 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 179 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-116

Anambra-20

FCT-9

Oyo-9

Rivers-9

Delta-3

Nasarawa-3

Edo-2

Kaduna-2

Ogun-2

Plateau-2

Ekiti-1

Osun-1

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 60,834 sai kuma mutum 52,143 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1116 suka riga mu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Iyaye, dalibai na rokon El-Rufa'i ya bude makarantu a jihar

Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834
Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834 Credit: @NCDC
Asali: UGC

KU KARANTA: An bayyana ranar buɗe makarantun gaba da sakandare a jihar Kano

A wani labarin mai tashe, gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana'o'i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel