An damƙe wanda ya maye gurbin Gana

An damƙe wanda ya maye gurbin Gana

- Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama Kumaor Fachii wanda ya maye gurbin Terwase Akwaza wato Gana

- Sojojin sun kamo Fachii da ake yi wa lakabi da Kwamanda a gidan budurwarsa da ke karamar hukumar kauyen Agbi a karamar hukumar Katsina-Ala a Benue

- Rundunar sojin ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba sai da ga bayan dukkan 'yan kungiyar fashin na Gana muddin ba su tuba sun mika wuya ba

Rundunar sojojin Nigeriya ta kama Kumaor Fachii, da aka fi sani da Kwamanda wadda shine mataimakin gaggarumin dan fashi marigayi Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.

Kwamandan runduna ta musamman ta hudu, ƙaramar hukumar Doma ta jihar Nassarawa, Manjo Janar Ali Gadzama Mounde ne ya yi holen sa a Doma.

An damƙe mataimakin Gana
Sojoji sun kama mataimakin Gana. Hoto @PremiumTimesng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Mounde ya ce an kama Fachii a gidan budurwar sa da ke ƙauyen Agbi a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi, ya ce, "Na gayyace ku nan wurin kwanaki 36 da suka gabata lokacin da muka yi holen Terwase Akwaza aka Gana. Na ce wasu daga cikin yaransa sun tsere kuma muna neman su.

"Mun kama mataimakin Gana, wannan shine Fachii wanda aka fi sani da Kwamanda, mataimakin Gana, wadda ya gaji tsafinsa.

"Na gabatar muku da shi ki gani cewa zamu cigaba da aikin mu har sai sun tuba sub dena laifuka.

"Shine mutum na 76 da muka kama bayan Gana yayin da hudu sun mutu," in ji shi.

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

A cewar sa abubuwan da aka ƙwato hannun wanda ake zargin su hada da bindiga, harsashi, khakin sojoji, layyu da guru da sauransu.

Janar Mounde ya ce sojojin na kokarin ganin sun kama yan kungiyar Gana su 400 a jihar Benue da kewaye.

Wanda ake zargin ya ce, "Na amsa cewa ni ɗan kungiyar Gana ne, amma ba ni bane mataimakin sa.

"Acaba ba ke yi kafin na shiga ƙungiyar Gana a 2018. Na yi garkuwa da mutane da dama.

"Marigayi Gana ya mika ƙungiyar hannun ƙaninsa Azonto, wadda har yanzu yana cikin daji," in ji shi.

An kashe Gana a jihar Benue a watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel