Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

- Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya naɗa ɗan ƙabilar Ibo a matsayin hadimansa

- Gwamna Yahaya ya naɗa Prince Chidebelu Cornelius Ewuzie a matsayin mashawarci kan harkokin inganta alaƙa tsakanin al'umma

- Gwamnan ya ce inganta alaƙa tsakanin mabanbantan mutane lamari ne mai muhimmanci da ya dace a mayar da hankali kansa don cigaban ƙasa

Gwamnan Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa
Gwamna Muhammadu Inuwa. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya naɗa wani Ibo, Prince Chidebelu Cornelius Ewuzie a matsayin mashawarcinsa na musamman kan inganta alaƙa tsakanin garuruwa.

Da ya ke jawabi yayin bikin rantsar da su a gidan gwamnati a Gombe a ranar Laraba 14 ga watan Oktoba, gwamnan ya ce alaƙa tsakanin garuruwa lamari ne da ya kamata a bawa muhimmanci don cigaba ƙasa.

Gwamna Yahaya ya kuma rantsar da Peter Bitrus Bilal a matsayin mashawarcin na musamman kan cigaba da aiwatar da ayyuka.

Gwamnan Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa
Gwamna Muhammadu Inuwa da sabbin hadimansa. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wasu sun samu biliyoyin naira da zanga-zangar EndSars, in ji ɗan gwagwarmaya, Sowore

Ya taya wadanda aka naɗa mukami mulkin ya kuma bukaci suyi amfani da kwarewar su don kawo cigaba a jihar.

A bangarensa, Prince Ewuzie da aka fi sani da Chimack ya yi wa gwamnan godiya bisa nadin da ya yi musu.

Ya bawa gwamnan tabbacin cewa za su yi masa biyayya kana za su dage don ganin sun kawo cigaba a jihar.

Gwamnan Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa
Gwamna Muhammadu Inuwa yayin rantsar da sabbin hadimai. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

A wani rahoton, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.'

Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel