Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa

Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa

- CNG tace zata fara zanga-zanga maras tsayawa daga ranar Alhamis mai zuwa akan matsalolin dake addabar Arewacin Najeriya

- Tace ta lura da yadda shugaban kasa da gwamnonin arewa suka zura wa 'yan arewa ido sunata fama da bala'o'i iri-iri

- Tace jihohin arewa na fama da matsanancin rashin tsaro, ga kuma matsalar rashin daidaitawar malamai da gwamnati

CNG tace zata fara zanga-zanga maras tsayawa daga ranar Alhamis mai zuwa, akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar tace, za ta yi hakan ne don sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin halin da jihohin arewa 19 suke ciki.

CNG tace, gwamnonin arewa sun gaza akan bai wa rayuka da dukiyoyin 'yan arewa cikakken tsaro, don haka tura ta kai bango.

Ba a harkar tsaro kadai gwamnonin suka kasa ba, har da karin kudi akan asalin kudin wutar lantarki.

Kamar yadda CNG tace, ta fahimci cewa shugaban kasa da gwamnoni basa yin wani kokari wurin daidaitawa da malaman jami'a.

CNG ta kula da yadda harkar tsaro ta lalace a arewa, kuma gwamnati bata yin komai akai.

Ta kara cewa, shugaban kasa ya kalmashe hannu ya zura wa dubbannin 'yan Najeriya ido, 'yan bindiga suna ta wahalar dasu.

KU KARANTA: EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so

Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa
Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan ganawar Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai a Kaduna

A wani labari na daban, mutum biyar da ake zargi da fashi da makami wadanda suka boye ta karkashin inuwar zanga-zangar matasa sun shiga hannun jami'an tsaro.

Ana zargin mutum biyar din da fashi da makami a cikin cunkoson jama'an da ke zanga-zanga. Wadanda ake zargin sune Olasunkami Oyewole, Quadri Lawal, Abraham Olateju, Tunde Bello da Olagoke Adewole.

Dukkansu sun shiga hannu a yankin Ketu da ke Legas. Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, wanda ya sanar da hakan a ranar Talata, ya ce rundunar ta wakilta wasu jami'anta wadanda za su damko mata masu cin zarafi tare da fashi a cunkoson ababen hawa a Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel