Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Katsina (Bidiyo)

Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Katsina (Bidiyo)

- Hedkwatar tsaron Najeriya DHQ ta alanta nasarar sojin sama a jihar Katsina

- A harin da aka kai jiya, Sojin sun hallaka dimbin yan bindigan tare da ragargaza sansaninsu

- Sojin sun samun labarin kasancewar yan bindigan a wajen ne daga bakin mutane

Rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) karkashin atisayen Operation HADARIN DAJI sun samu nasarar ragargaza wani sansanin yan bindigan da suka addabi al'ummar jihar Katsina da kewaye

Jami'an sun samu nasarar yin hakan ne a harin da suka kai ranar Talata, 13 ga Oktoba.

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa "an wargaza sansaninsu kuma an hallaka wasu yan bindigan kusa da Unguwar Ali-Kere a jihar Katsina."

A jawabin da hedkwatar ta saki a shafinta na Tuwita, ta ce "bayanai daga mutan gari ya nuna cewa akwai yan bindiga a wajen kuma sun kafa sansani."

"Saboda haka hukumar mayakan sama ta tura jiragen yaki da masu saukar angulu inda suka ragargaji wajen," jawabin ya kara.

KARANTA NAN: Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta

Kalli bidiyon harin:

KU DUBA: Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli

Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Katsina (Bidiyo)
Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Katsina (Bidiyo) Credit: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

A bangare guda, gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) tace zata fara zanga-zanga maras tsayawa daga ranar Alhamis mai zuwa, akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar tace, za ta yi hakan ne don sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin halin da jihohin arewa 19 suke ciki.

CNG tace, gwamnonin arewa sun gaza akan bai wa rayuka da dukiyoyin 'yan arewa cikakken tsaro, don haka tura ta kai bango.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel