Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta

Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta

- Mayakan Boko Haram na cigaba da kashe mutane yadda suka ga dama a jihar Borno

- A makon da ya gabata suka kashe mutane 14 masu noman rani a kauyen Ngwon dake Maiduguri

- Sun mamayi manoman ne, inda suka zagaye su ta yadda babu yadda za'a yi su gudu

A makon da ya gabata, gwamnatin jihar Borno ta fara kokarin mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwan su. Ma'aikatar gyara da mayar da 'yan gudun hijira gidajensu ce take jagorantar shirin.

AFP ta ruwaito yadda mayakan Boko Haram suka shiga gonaki kuma suka farma masu noman rani a kauyen Ngwon, wanda yake da tazarar kilomita 14 ta Arewa zuwa birnin Maiduguri.

'Yan Boko Haram din sun yanka wuyan manoman kuma sun yi musu alama ta masu jihadin Musulunci.

"Sun yanka manoman, har suka yi sanadin mutuwar guda 14, daya kuma ya tsira da ransa amma da munanan raunuka, sai suka bar shi ya karasa mutuwa," a cewar Babakura Kilo, shugaban 'yan sa kai.

Wani Ibrahim Liman, dan sa kai, yace sun mamayi manoman ne, inda suka zagayesu ta yadda ba za su iya guduwa ba.

Liman yace mutum 1 da ya rayu yana nan a asibiti, rai a hannun Allah.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari birnin Kano, sun ragargaza wurare 3 a rana daya

Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta
Sabon harin Boko Haram: Rayukan manoma 14 sun salwanta. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Babu jinin dan Najeriya da ya cancanci zuba - Goodluck Jonathan

A wani labari na daban, wani mutum dan Najeriya, shugaban kamfanin tsaro na Fionet, yace , don ya koya wa dansa, Uyiogosa makamar sana'a da kuma zama masa uba nagari, ya daukesa aiki a kamfaninsa.

Yayin da yayi wallafarsa a LinkedIn, ya wallafa hoton dansa sanye da kayan masu gadi. A yadda ya wallafa, ya jefa wa iyaye tambaya, akan idan zasu iya koyawa yaransu sana'arsu ko kuma zasu barsu hakanan kada su wahala?

Felix ya godewa Ubangiji da ya bashi damar taso da yaronsa cikin tarbiyya don su zama 'ya'yan da zasu jagoranci al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel