Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu

Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu

- Gwamnan jihar legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa za ta rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi

- Ya sanar da hakan ne yayin wani jawabi da yayi ga masu zanga-zanga a gaban majalisar jihar Legas

- Ya ce tuni ya ware miliyan 200 tare da bibiyar hada sunayen wadanda aka kashe din domin rage wa iyalansu radadi

Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas ya ce gwamnatin jihar ta ware kudi har naira miliyan 200 domin biyan diyya ga iyalan da jami'an rundunar SARS suka kashe musu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga masu zanga-zangar a gaban majalisar jihar Legas a ranar Talata.

Sanwo-Olu ya ce an ware kudaden ne domin tallafa wa iyalan wadanda 'yan sandan suka kashe bisa kuskure.

Ya ce an samo jerin sunayen wadanda 'yan sandan suka kashe kuma ana sake bincikawa domin tabbatar da cewa ba a cire sunan kowa ba.

"Mun ware kudi har naira miliyan 200 saboda wadanda aka kashe," yace.

Gwamnan ya kara da tabbatar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter bayan ganawar da yayi da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a Abuja.

Ya ce za a mika kudaden ga jama'a da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

"A Legas, mun kafa wani kwamiti na jama'a da kungiyoyi masu zaman kansu domin rage radadi ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu ga cin zarafin 'yan sanda," wallafar tace.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja

Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu
Mun ware N200m domin rage wa iyalan wadanda aka kashe radadi - Sanwo-Olu. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya nuna damuwarsa a kan rikicin da ke cigaba da barkewa a sassan kasar nan. Ya yi kira ga matasa da su ajiye makamansu tunda sun yi nasara.

Bello, wanda yayi wannan kira ga matasan da ke zanga-zanga a kan bukatar kawo gyara a ayyukan 'yan sanda, ya ce tuni matasan Najeriya suka yi nasara amma kada su bari nasarar ta subuce musu.

Gwamnan ya ce ya matukar damuwa da yadda suke zanga-zangar wanda ya fara cikin lumana amma ya zama wani abu daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel