Mutanen Zuru mazauna Kaduna sun yi wa marigayi Shehu Idris addu'a ta musamman

Mutanen Zuru mazauna Kaduna sun yi wa marigayi Shehu Idris addu'a ta musamman

- Ƴan asalin garin Zuru daga jihar Kebbi mazauna jihar Kaduna sun yi addu'a ta musamman ga marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

- An yi addu'ar ne a fadar Wakilin Zuru da Kewaye Injiniya Zubairu da ke unguwar Mahuta a Kaduna

- Al'ummar na Zuru da suka hada da musulmi da kirista sunyi addu'ar Allah ya jiƙan Shehu Idris da suka ce tamkar uba ne a wurinsu kuma suka shawarci sabon sarki ya yi koyi da halinsa na son zaman lafiya

Mutanen Zaria sun yi wa marigayi Shehu Idris addu'a ta musamman
An yi wa marigayi Shehu Idris addu'a ta musamman a Zaria. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

Ƴan Zuru daga jihar Kebbi mazauna jihar Kaduna sun yi addu'a ta musamman ga marigayi Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumban 2020.

Ƴan Zurun sun bayyana marigayi Sarkin a matsayin uba, sun kuma bukaci sabon sarkin, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi koyi da halayen tsohon sarkin musamman na kira ga zaman lafiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa musulmi har ma da Kirista daga Zuru sun hallarci taron da aka yi a fadar Wakilin Zuru da Kewaye, Injiniya Zubairu Kabiru a unguwar Mahuta da ke Kaduna.

KU KARANTA: Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus

Malam Mas'ud Abdulkarim ne ya yi addu'ar musulmi yayin da Fasto Ayuba Yusuf ya jagoranci addu'ar Kirista inda dukkansu suka roki Allah ya gafarta wa marigayin.

Wakilin Zuru da Kewaye, Injiniya Kabir ya ce, "Mutuwarsa ta girgiza dukkan mu ƴan kabilar Zuru mazauna Kaduna domin tamkar Uba ya ke gare mu kuma mutum ne mai son zaman lafiya.

"Ya kasance a koda yaushe yana umurtar mu mu zauna lafiya da kowa a unguwannin mu da kasa baki ɗaya."

A wani labarin, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.'

Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel