Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa ta yanar gizo (Hotuna)
- Kamar yadda aka saba kowani Laraba, an yi zaman majalisar fadar Buhari
- Yayinda wasu ministoci ke hallare a fadar, sauran na magana ta yanar gizo
Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa ta yanar gizo na 19 ranar Laraba, 14 ga Oktoba, a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.
An fara zaman misalin karfe 10 na safe.
Wadanda ke hallare cikin fadar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Ibrahim Gambari; dake mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Munguno.
Daga cikin ministocin dake cikin fada akwai Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed; Ministar Kudi, Zainab Shamsuna; Ministan Shari'a, Abubakar Malami; Ministan ayyuka, Raji Fashola; da ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami.
Sauran sun hada da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Ministan Sufurin jirgin sama, Hadi Sirika; Ministan harkokin cikin gida, Raud Aregbesola; Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire; da mininstan wuta, Saleh Mamman.
Ministocin da suka halarta ta yanar gizo sun hada da Ministan harkokin waje, Geofreey Onyeama; karamar ministar masana'antu, Maryam Katagum; Ministar harkokin mata, Pauline Tallen; dss.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Bamu amince a bude makarantu ba - Malaman Poly sun alanta

Asali: Twitter
KU KARANTA: Ayyukan da gwamnati za ta yi da N3.85tr a shekarar badi – Zainab Ahmed

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng