EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so

EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so

- Ahmad Lawan, Shugaban majalisar dattawa ya ce zanga-zangar da matasa suka yi kwalliya ta biya kudin sabulu

- Ya bukaci matasan da ke zanga-zangar kawo karshen runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami da su hakura haka

- Shugaban majalisar dattawan ya ce tunda gwamnati ta duba bukatunsu, bai dace su cigaba da zanga-zanga ba

Shugaban majalisar dattawa ya ce zanga-zangar da ta barke a fadin kasar nan a kan cin zarafi da zaluncin da 'yan sanda ke yi, kwalliya ta biya kudin sabulu.

Bayan zanga-zangar a sassan kasar nan, Mohammed Adamu ya sanar da rushe runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami a ranar Lahadi, amma masu zanga-zangar sun ki barin tituna.

A yayin jawabi a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, Lawan ya ce babu bukatar cigaba da zanga-zangar tunda an rusa rundunar.

Shugaban majalisar dattawa ya ce a bai wa gwamnati damar hukunta tsohuwar rundunar da ake zargi da cin mutunci da zarafin jama'a tare da take musu hakki.

Shugaban ya ce, "Abinda jami'an SARS ke yi bai dace ba kuma ba za a lamunci hakan ba. Amma a tunani na kwalliya ta biya kudin sabulu kuma an samu abinda ake so.

"Babu bukatar a cigaba da zanga-zangar bayan an rushe rundunar kuma za a hukunta masu hannu a laifukan. A tunani na ya kamata mu bai wa gwamnati damar tabbatar da abinda tayi ikirarin ta zartar.

"Yan Najeriya suna da hakkin yin zanga-zanga. Gwamnati ta sauraresu kuma ta dauka mataki."

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci

EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so
EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel