Bamu amince a bude makarantu ba - Malaman Poly sun alanta

Bamu amince a bude makarantu ba - Malaman Poly sun alanta

- Bayan mako daya da barazanar tafiya yajin aiki, malaman ASUP sun gana da ministan Ilimi

- Malaman na kokarin bin sahun takwarorinsu na jami'o'i da suka kwashe watanni bakwai suna yaji

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba, ya gana da shugabannin kungiyar malaman makarantun fasaha wanda akafi sani da Poly (ASUP) ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Nwajuiba ya zanna da su domin ganin yadda za'a shawo kan matsaloli kuma kada su shiga yajin aiki.

Za ku tuna cewa kungiyar ASUP ta baiwa gwamnatin tarayya kwanaki 21 ta magance wasu matsalolin da ta gindaya ko kuwa su shiga yaji kaman takwarorinsu na jami'a.

Tawagar ASUP karkashin jagorancin shugabanta, Anderson Ezeibe, ya bayyana matsalolin da malaman suka dade suna jurewa tun kan bullar cutar COVID-19.

Ya bayyanawa Nwajuiba cewa gaskiyar magana itace makarantun fasaha basu shirya komawa karatu ba saboda ba'a cika dukkan sharrudan da kwamitin yaki da cutar Korona ta gindaya ba.

A cewar Ezeibe, mambobin ASUP suna nadamar rijista a manhajar biyan albashi ta IPPIS saboda matsalolin da suke fuskanta wanda ya hada da rashin biyan wasu albashi da rashin bada daman gyara cikin isasshen lokaci.

Ya kara da cewa ana cin zarafin mambobinsu da sukayi fito-na-fito da gwamnati a baya, musamman ma'aikatan kwalegin fasaha IMT dake Enugu, da kuma ma'aikatan Bida Poly biyu da aka sallama ba tare da hujja mai karfi ba.

DUBA NAN: Akalla mutane 10 sun mutu a zanga-zangar #ENDSARS kawo yanzu

Bamu amince a bude makarantu ba - Malaman Poly sun alanta
Kadpoly Credit: factchecknews.com
Asali: UGC

DUBA NAN: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun yarje a rage farashin lantarki na watanni 3

A makon da ya gabata, mun ruwaito muku cewa manyan ma'aikatan makarantun fasaha a Najeriya watau Poly sun yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalolin da suke fuskanta game da manhajar biya albashi ta IPPIS.

Ma'aikatan karkashin kungiyar manyan ma'aikatan makarantun fasaha a Najeriya SSANIP, sun yi ganawar gaggawa a hedkwatar kungiyar kwadago 'Labour House' dake birnin tarayya Abuja.

Sun bayyana rashin amincewarsu da yadda hukumar kula da makarantun fasaha na kasa NBTE ke gudanar da wasu ayyukanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel