EndSARS: Kun riga kun samu nasara, kada ku bari ta subuce - Yahaya Bello

EndSARS: Kun riga kun samu nasara, kada ku bari ta subuce - Yahaya Bello

- Gwamna Yahaya Bello ya yi kira da babbar murya ga matasan masu zanga-zangar Endsars

- Gwamnan jihar Kogin ya ce da matasan kamata yayi su ajiye makamansu tunda sun yi nasara

- Kamar yadda yace, gwamnati ta rushe rundunar SARS kuma za ta hukunta jami'ai masu zalunci

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya nuna damuwarsa a kan rikicin da ke cigaba da barkewa a sassan kasar nan. Ya yi kira ga matasa da su ajiye makamansu tunda sun yi nasara.

Bello, wanda yayi wannan kira ga matasan da ke zanga-zanga a kan bukatar kawo gyara a ayyukan 'yan sanda, ya ce tuni matasan Najeriya suka yi nasara amma kada su bari nasarar ta subuce musu.

Gwamnan ya ce ya matukar damuwa da yadda suke zanga-zangar wanda ya fara cikin lumana amma ya zama wani abu daban.

Ya ce shugabanni sun ji kiran matasan wanda hakan yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rushe runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami tare da daukar alkwarin kawo gyara a ayyukan 'yan sanda.

Bello ya ce lokaci yayi da Matasan da ke zanga-zanga a fadin kasar nan za su yada makamai sannan su yi magana a gane abinda suke bukata.

"Ni da jama'ata da muke wa matasa fatan alheri mun matukar damuwa da yadda rikici ke cigaba da barkewa. Mun ga yadda rikicin ya karu a wurare da yawa tun daga ranar Talata.

"Mun damu da yadda zanga-zangar lumana take neman komawa wani abu daban. An fara harar kayayyakin gwamnati tare da yaki da 'yan sanda.

"Ni a ganina kun yi nasara kuma dole ne in yi kira gareku da kada ku bari ta subuce muku. Masu zanga-zangar sun samu babbar nasara kuma hikima ce idan kuka bata kariya," yace.

KU KARANTA: SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

EndSARS: Kun riga kun samu nasara, ku yada makamanku - Yahaya Bello
EndSARS: Kun riga kun samu nasara, ku yada makamanku - Yahaya Bello. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel