EndSARS: 'Yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da fashi a cikin cunkoso a Legas

EndSARS: 'Yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da fashi a cikin cunkoso a Legas

- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wasu mutum 5 da ake zargi da fashi da makami

- Ana zargin matasan da yin amfani da zanga-zangar da ake yi domin fashi da makami

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya tabbatar da kamen matasan

Mutum biyar da ake zargi da fashi da makami wadanda suka boye ta karkashin inuwar zanga-zangar matasa sun shiga hannun jami'an tsaro.

Ana zargin mutum biyar din da fashi da makami a cikin cunkoson jama'an da ke zanga-zanga.

Wadanda ake zargin sune Olasunkami Oyewole, Quadri Lawal, Abraham Olateju, Tunde Bello da Olagoke Adewole. Dukkansu sun shiga hannu a yankin Ketu da ke Legas.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, wanda ya sanar da hakan a ranar Talata, ya ce rundunar ta wakilta wasu jami'anta wadanda za su damko mata masu cin zarafi tare da fashi a cunkoson ababen hawa a Legas.

Ya ce mutum biyar da ake zargi da fashi da makami sun shiga hannun 'yan sandan yankin Ketu bayan sun yi wa wasu mutum biyu fashi a babban titin Legas zuwa Ibadan.

Odumosu, wanda yayi amfani da damar wurin kira ga jami'an tsaro a kan cewa su dage wurin cafko duk 'yan ta'addan da ke tada wa 'yan Najeriya hankali.

Ya yi kira ga jami'an tsaron da su dage wurin samar da tsaro ga kowa duk da zanga-zangar da ake cigaba da yi a fadin jihohin kasar nan.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu

EndSARS: 'Yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da fashi a cikin cunkoso a Legas
EndSARS: 'Yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da fashi a cikin cunkoso a Legas. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel