Hotuna: Ango ya garzaya wurin zanga-zangar EndSars daga wurin ɗaurin aurensa
- Wani ango a Najeriya ya tafi wurin zanga-zangar EndSars a ranar da aka ɗaura masa aure ko kaya bai canja ba
- Angon ya wallafa hotunan sa sanye da kayan da aka ɗaura masa aure ɗauke da takarda da cewa 'ku rushe rundunar SARs yanzu'
- Matasa da dama a jihohi daban-daban a Najeriya sun kwashe kwanaki suna zanga-zangar neman ganin an rushe SARs tare da yin wasu sauye-sauye a rundunar ƴan sanda

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Wani ɗan Najeriya ya shiga ya zanga-zangar da matasa suka yi a kasar na neman rushe rundunar ƴan sanda ta musamman na SARs a ranar da aka ɗaura masa aure a Legas.
An ɗauki hotunan mutumin mai suna @OgebeniKunle1 a Twitter sanye da kayan da ya tafi wurin ɗaurin aure da su a jikinsa yana rike da takarda ta zanga-zanga.
DUBA WANNAN: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

Asali: Twitter

Asali: Twitter
KU KARANTA: Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus
Hakan na nuna akwai alamun bayan ɗaurin auren bai wuce ko ina ba sai wurin zanga-zangar domin shima ya bada tasa irin gudummawar.
A hotunan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya rubuta cewa: "A yau na shiga zanga-zangar #EndSARS bayan an ɗaura min aure a kotu. Kada SARS su kashe wa matata mijin ta."
A wani labarin daban, mutum tara ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, a jihar cikin wata sanarwa da ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 9 na safe da ya ritsa da mota da adaidaita sahu a hanyar Kano zuwa Zaria a kauyen Imawa da ke karamar hukumar Kura.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng