Zulum ya amince a dauki sabbin malamai 776 a Borno

Zulum ya amince a dauki sabbin malamai 776 a Borno

- Gwamnan Borno Babagana Zulum ya amince a ɗauki sabbin malaman makaranta 776 a jiharsa

- Gwamna Zulum ya kuma ce Majalisar Zartarwa na jihar za ta tsawaita wa malaman gaba da sakandare shekarun aiki kafin ritaya

- Babagana Zulum ya ce gwamnatin za ta yi duk mai yiwuwa don dawo da darajar da ilimi ya ke da shi a jihar

Zulum ya amince a dauki sabbin malamai 776 a Borno
Babagana Zulum. Hoto daga www.pulse.ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Gwamnan da yace malamai su koma aiki ranar 1 ga watan Nuwamba ya kara da cewa za a bada umurnin ɗaukan sabbin malamai nan take bayan kammala aikin tantance su da ake a jihar.

KU KARANTA: Ana fargabar mutum 10 sun mutu, 30 sun jikkata sakamakon hatsarin da treloli biyu suka yi a Adamawa

Gwamnan ya kuma ce Majalisar Zartarwa na jihar ta yanke shawarar tsawaita shekarun murabus na malaman makarantun gaba da sakandare a jihar inda ya ce tuni an tura wa majalisar jihar ƙudurin.

Zulum ya bawa ma'aikatar umurnin ƙara ɗaukan malaman darussan kimiyya na wuccin gadi don cike giɓin da ake da shi.

Gwamnan ya jadadda aniyar gwamnatinsa na ganin ta dawo da darajar ilimi a jihar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar. Mohammed Aliyu Soba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel