Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar J.P. Clark

Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar J.P. Clark

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Farfesa J.P. Clark ga iyalansa, gwamnati da al'ummar Delta da marubuta a Najeriya

- Buhari ya bayyana marigayin shararren marubucin a matsayin dan kishin kasa da rubuce-rubucen da ya wallafa za su cigaba da zama fitila da marubuta a Najeriya

- Shugaban kasar ya yi addu'ar Allah ya gafartawa marubucin da ya ce mutuwarsa ya bar babban gibi da zai yi wuyar cikewa

Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar J.P. Clark
Marigayi Emeritus Farfesa J.P. Clark
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar fitaccen marubuci Emeritus Farfesa John Pepper Clark cikin sakon ta'azziyar da ya aike wa iyalan Clark-Fudulu Bekederemo a madadin gwamnatin tarayya.

Shugaba Buhari cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya yi bajinta a fanin rubuce-rubuce wanda ayyukansa da ya wallafa suka janyo masa mutunci da girmamawa daga gida Najeriya da ma kasashen waje.

KU KARANTA: Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

Buhari ya ce rasuwar Farfesa J.P. Clark babban rashi ne ga duniyar marubuta amma kuma shugaban kasar ya ce "rubuce-rubucensa da suka saka ya shahara da gida da waje za su cigaba da zaburar da marubutan Najeriya su rika kokarin ganin sun kware a bangaren.

"Shugaban kasar ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mammacin dan kishin kasa, gwamnati da al'ummar jihar Delta da marubuta a kasar baki daya."

"Ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin."

A wani labarin daban, Ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa - Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel