Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari sun kashe mutane takwas

Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari sun kashe mutane takwas

- Ƴan bindiga daɗi sun kai hari ƙauyen Shau da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina

- Yayin harin sun hallaka a ƙalla mutane takwas sun kuma ƙone gidajen al'umma bayan sace musu kayan abinci

- Daga bisani jami'an tsaro sun amsa kirar mazauna ƙauyen sun iso sun fatattaki ƴan bindigan sun gudu cikin daji

Ƴan bindiga a ranar Lahadi sun kai hari ƙauyen Shau a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina inda suka kashe a ƙalla mutum takwas.

Mazauna garin sun ce ƴan bindigan sun ƙone gidaje masu yawa a kauyen sannan sun sace kayan abinci da wasu kayyakin.

The Punch ta ruwaito cewa ƴan bindigan har ila yau sun lalata motar dagajin ƙauyen.

An ruwaito cewa wannan harin ya saka mutane da dama sun tsere zuwa ƙauyukan da ke makwabtaka da su.

Jami'an tsaro na haɗin gwiwa da suka amsa kirar mazauna ƙauyen sun yi bata kashi da ƴan bindigan sun kora su cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo ya tabbatar da afkuwar harin.

KU KARANTA: Iyan Zazzau Bashir Aminu ya maka El-rufai a kotu saboda nada Bamalli sarki

Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari sun kashe mutane takwas
Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari sun kashe mutane takwas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

A wani labari na daban, ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa - Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce sun ciro gawarwaki 10 da kuma wasu mutum 30 da suka samu rauni bayan tirelolin biyu da ke gudu sun yi karo.

Jami'an hukumar FRSC a Mayobelwa sun tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin da suka ce gudu fiye da kima ya janyo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel