FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista

FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista

- Ministan noma, Muhammad Nanono yace gwamnatin tarayya za ta kirkiri ayyuka miliyan 10 a karkashin ma'aikatarsa ta noma

- Ministan ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi dashi akan shirin ranar Abinci ta duniya dake gabatowa a ranar 16 ga watan Oktoba

- A cewarsa, fiye da 'yan Najeriya miliyan 1 sun amfana da bashi mara ruwa da gwamnatin tarayya ta bai wa manoma a shekarar 2020

Gwamnatin tarayya zata kirkiri ayyuka miliyan 10 a fannin noma da kiwo ta shirin noma don abinci da samun ayyuka (AFJP).

Ministan noma, Muhammad Nanono ya fadi hakan a ranar Talata a Abuja lokacin da ake wata tattaunawa da shi akan shirye-shiryen murnar ranar Abinci ta duniya dake gabatowa.

Ana murnar ranar abinci ta duniya ne a duk ranar 16 ga watan Oktoba a kasashe fiye da 150 don tayar da matsalolin fatara da yunwar dake addabar mutane a duniya.

Ministan yace AFJP daya ne daga cikin shirin da shugaban Muhammadu Buhari yayi a watan Yuli, don habakar da noma da kuma bai wa manoma bashi ba tare da amsar ruwa ba.

A cewarsa, "Mutane miliyan 1.1 ne suka amfana da bashin a Abuja da sauran jihohin Najeriya."

Ya kara da cewa, duk da an so tsarin AFJP ya amfana mutane miliyan 5, ma'aikatar noma ta ba manoma 1,138,000 bashi a cikin jihohi 36 da Abuja a karon farko.

Ministan yace wannan gwamnatin na tsaye tsayin-daka don ganin ta bunkasa harkar noma a kasar.

KU KARANTA: Da duminsa: IGP ya kirkiri rundunar SWAT domin maye gurbin SARS

FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista
FG za ta samar da ayyuka miliyan 5 a bangaren aikin noma - Minista. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci

A wani labari na daban, dangane da zaben 2023 dake tunkarowa, Hauwa Atiku Uwais, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tayi alkawarin mara wa mahaifinta baya, indai har ya sake neman takarar shugaban kasar Najeriya.

Hauwa ta bayyana hakan ne jiya a Abuja, lokacin da ake wata tattaunawa akan yadda za'a kawo gyara da cigaban Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel