Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci

Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci

- Gwamnatim jihar Nasarawa ta dakatar da babban hadimin gwamnan jihar, Stanley Buba a ranar 9 ga watan Oktoba akan zarginsa da ha'inci

- Wannan hukuncin ya biyo bayan zarginsa da amfani da matsayin MD din NUDB wurin bayar da alamar biyan kudin shigar filaye a jihar

- Bayan dakatar dashi, Sakataren gwamnatin jihar, Bar. Aliyu Ubandoma ya umarci Buba da ya gabatar da duk wasu kayan gwamnati dake hannunsa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya amince da dakatar da babban hadiminsa na musamman, Stanley Buba, akan yaudara da ha'inci.

Majalisar jihar, ta bukaci dakatar da Buba sakamakon zarginsa da amfani da matsayin MD din NUDB wurin bayar da alamar biyan kudin shigar filaye.

Shugaban majalisar ya umarci wani dan kwamitin rikon kwarya da yayi bincike akan al'amarin.

Bayan gabatarwa da Buba wasikar dakatar da shi daga aiki a ranar 9 ga watan Oktoba, sakataren gwamnatin jihar, Bar. Aliyu Ubandoma, ya umarci Buba da ya gabatar da duk wasu kayan gwamnati dake hannunsa a matsayinsa na ma'aikaci.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu

Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci
Da duminsa: Gwamnan Sule ya sallami hadiminsa a kan zargin ha'inci. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel