Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus

Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus

- Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya zaɓaɓen mataimakinsa, Lucky Ayedatiwa sun ziyarci Buhari a Abuja

- Akeredolu ya ziyarci shugaban ƙasar ne don ya gabatar masa da takardar shaidan cin zaɓe da INEC ta bashi

- Gwamnonin jihar Legas, Jigawa, Kebbi, Ekiti da Yobe sun yi wa Akeredolu rakiya wurin ganawa da Buhari

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar Talata ya ziyarci Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Akeredolu wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamna da aka yi a jiharsa ta Ondo a ranar Asabar da ta gabata ya yi amfani wannan damar don nuna wa shugaban kasa shaidar cin zabensa.

Zaɓaɓɓen mataimakin gwamnan jihar, Lucky Ayedatiwa da gwamnonin jihohin Legas, Kebbi, Ekiti da Jigawa sun masa rakiya.

KU KARANTA: Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari

A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamanti bayan ganawarsa da Buhari, Akeredolu ya yi kira ga mataimakinsa na yanzu, Agboola Ajayi ya yi murabus idan har akwai sauran dattaku tare da shi.

A baya, The Punch the ruwaito cewa gabanin zaɓen, Ajayi ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP sannan ya koma ZLP.

Ya yi takarar zaɓe a ƙarƙashin ZLP a zaben gwamnan da aka yi a jihar inda ya zo na uku.

Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus
Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus. Hoto daga @BuhariSallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ana fargabar mutum 10 sun mutu, 30 sun jikkata sakamakon hatsarin da treloli biyu suka yi a Adamawa

Gwamnan ya ce ko da Ajayi bai yi murabus ba sauran kwanaki kaɗan ya sauka tunda za a rantsar da sabon mataimaki nan ba da daɗewa ba.

Akeredolu ya kuma janye maganar da ya yi na cewa wasu ƴan jihar maƙiyansa ne har abada inda yace bayan cin zaɓe yanzu kowa nashi ne.

Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus
Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus. Hoto daga @BuhariSallau1
Asali: Twitter

A wani labari na daban, hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bawa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da mataimakinsa Lucky Ayedatiwa takardar shaidar cin zaɓe.

Kwamishinonin zaɓe na jihar Ondo, Ambasada Rufus Akeju ne ya bawa Akeredolu takardar shaidar a hedkwatar hukumar da ke Akure, babban birnin jihar a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel