Da duminsa: IGP ya kirkiri rundunar SWAT domin maye gurbin SARS

Da duminsa: IGP ya kirkiri rundunar SWAT domin maye gurbin SARS

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya kirkiri sabuwar rundunar 'yan sanda

- Ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru wacce aka kira da SWAT domin maye gurbin SARS

- Sifeta janar na 'yan sandan ya ce za a duba lafiyar jiki tare ta kwakwalwar dukkan jami'an kafin a fara horarwa

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DCP Frank Mba ya sanar a ranar Talata a Abuja, ya ce duk jami'an 'yan sanda daga yankin kudu maso gabas da kudu-kudu za a horar da su a kwalejin yaki da ta'addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Ribas.

Wadanda ke rundunar daga arewaci da kuma kudu maso yamma za a horar da su a kwalejin horar da 'yan sanda da ke Nasarawa da ta Ila-Orangun, jihar osun.

Takardar ta kara da bayyana cewa, umarni daga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya shine dukkan jami'an SARS su bayyana a hedkwatar 'yan sanda da ke Abuja domin gwajin lafiya da kwakwalwa.

KU KARANTA: Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

Da duminsa: IGP ya kirkiri rundunar SWAT domin maye gurbin SARS
Da duminsa: IGP ya kirkiri rundunar SWAT domin maye gurbin SARS. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar legas ta ce masu zanga-zanga sun harba jami'anta uku a ranar Litinin.

Jaridar The Cable ta wallafa yadda masu zanga-zanga suka rufe titunan Lekki, Surulere da Ikeja a jihar Legas inda suke bukatar a gyara tsarin ayyukan 'yan sanda.

Bayan zanga-zangar matasa a dukkan fadin kasar nan, Mohammed Adamu, Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya ya sanar da rushe rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel