Ba zamu yarda ba, sai ka janye - Sanatocin PDP kan nadin hadimar Buhari matsayin kwamishana a INEC

Ba zamu yarda ba, sai ka janye - Sanatocin PDP kan nadin hadimar Buhari matsayin kwamishana a INEC

- Nadin hadimarsa da Buhari yayi matsayin kwamishana a INEC ya bar baya da kura

- Sanatocin jam'iyyar hamayya sun ce Buhari ya saba alkawarin da yayi ranar da aka ranstar da shi

- Sun bukaci ya janye nadin saboda hakan ya sabawa dokar Najeriya

Sanatocin jam'iyyar hamayya a majalisar dattawa sun yi Alla-wadai da nadin Lauretta Onochie matsayin kwamishana a hukumar zabe ta kasa INEC da shugaba Buhari yayi.

Martani kan hakan, shugaban marasa rinjaye a majalisa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce nadin Lauretta ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

"Shugaba Buhari ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriyan da ya rantse zai kare da gayya ta hanyar nada Lauretta Onochie, " Yace

"Lamari na F, Sakin layi na 14, na 3rd Schedule na kundin tsarin mulkin kasa ya haramtawa wani dan jam'iyyar siyasa aiki a INEC."

"Marasa rinjaye a majalisar dattawa basu yarda da wannan nadi ba kuma suna kira ga shugaban kasa ya janye."

KARANTA WANNAN: Sanata Yusha'u Anka ya rigamu gidan gaskiya

Ba zamu yarda ba, sai ka janye - Sanatocin PDP kan nadin hadimar Buhari matsayin kwamishana a INEC
Lauretta Onochie @NweswireNGR/Tope Brown
Asali: Twitter

KU DUBA: Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Legit ta kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hadimarsa ta Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, a matsayin daya daga cikin kwamishanonin hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC.

Buhari ya gabatar da sunanta da wasu mutane uku gaban majalisar dattawa domin tantancesu da tabbatar da su.

Idan aka tabbatar da ita, Lauretta Onochie, wacce ta shahara da kare Buhari da zagin masu sukarsa a kafafen sada zumunta zata zama daya daga cikin alkalan zabe a Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da Buhari ya aike a zauren majalisar.

Sauran da Buhari ya aike da sunayensu sune Prof. Mohammed Sani mai wakiltan jihar Katsina; Prof. Kunle Ajayi mai wakiltan Ekiti, da nd Seidu Ahmed mai wakiltan Jigawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel