EndSARS: Dole ne a sallami shugabannin tsaro - Dattawan arewa

EndSARS: Dole ne a sallami shugabannin tsaro - Dattawan arewa

- Kungiyar dattawan arewa ta yi magana a kan zanga-zangar da ake yi akan SARS

- Kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauka mataki a kan 'yan sandan

- Ta yi kira ga shugaban kasar da ya yi wa aikin 'yan sanda garambawul tare da tsaron kasar baki daya

Kungiyar dattawan arewa (NEF) a ranar litinin ta bukaci garambawul ga tsarin 'yan sanda da kuma jami'an tsaro a fadin kasar nan.

Sun ce hakan zai fara ne da sallamar shugabannin tsaro tare da saka bukatun jam'a a kan gaba domin shawo kan mugun halin da kasar nan ke ciki.

Kungiyar a wata takarda da daraktan yada labaranta, Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya fitar ya ce ya zama dole a duba tsarin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami.

Takardar ta ce an bar 'yan arewa a cikin mawuyacin ta yadda 'yan bindiga, garkuwa da mutane da satar shanu suka yi kamari ba tare da an basu wata kariya ba.

"A bayyane yake idan aka ce akwai wasu abubuwa na rashin fahimta game da 'yan sandanmu da dukkan tsaronmu. Wasu suna zarginsu da zalinci yayin da wasu ke ganin kamar babu su kwata-kwata," yace.

Kungiyar ta ce hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari na rushe SARS da gyara tsarinsu, kamata yayi shugaban kasar ya sake duba tsarin 'yan sanda da na jami'an tsaro.

"Akwai cin zarafi kala-kala da ya kamata a duba sannan a shawo kansu amma an barsu ba tare da dubawa ba.

"Abun takaici ne yadda gwamnatin nan ke duba manyan al'amura da suka shafi tsaron kasa. Su kan jira har sai muguwar barna ta auku wanda hakan yake shafar nagarta da kuma kyan tsarin tsaro," tace.

KU KARANTA: SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

Dole ne a sallami shugabannin tsaro - Dattawan arewa
Dole ne a sallami shugabannin tsaro - Dattawan arewa. Hoto daga Dailysun
Asali: UGC

KU KARANTA: Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu

A wani labari na daban, dangane da zaben 2023 dake tunkarowa, Hauwa Atiku Uwais, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tayi alkawarin mara wa mahaifinta baya, indai har ya sake neman takarar shugaban kasar Najeriya.

Hauwa ta bayyana hakan ne jiya a Abuja, lokacin da ake wata tattaunawa akan yadda za'a kawo gyara da cigaban Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel