Gwamna Akeredolu ya karbi takardar shaidan cin zabe

Gwamna Akeredolu ya karbi takardar shaidan cin zabe

- Gwamnan jihar Ondo Akeredolu da mataimakinsa Ayedatiwa sun karbi takardar shaidar sake cin zaɓe daga hannun INEC

- Kwamishinan zaɓe na jihar Ondo, Rufus Akeju ne ya mika wa zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa takardar shaidar a ranar Talata

- Gwamnan ya sadaukar da nasararsa ga Allah da al'ummar jihar Ondo da suka fito suka zaɓe shi kwansu da ƙwarƙwata

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bawa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da mataimakinsa Lucky Ayedatiwa takardar shaidar cin zaɓe.

Kwamishinonin zaɓe na jihar Ondo, Ambasada Rufus Akeju ne ya bawa Akeredolu takardar shaidar a hedkwatar hukumar da ke Akure, babban birnin jihar a ranar Talata.

Gwamnan ya yaba wa INEC bisa nasarar gudanar da zaben na ranar Asabar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Zaben WTO: Ka taimaka ka yi min kamfen a wurin shugabannin duniya - NOI ta roki Buhari

Gwamnan wadda ya yaba wa ƙoƙarin hukumomin tsaro don tabbatar da anyi zaɓen lafiya ya sadaukar da nasararsa ga Allah da al'ummar jihar.

Gwamna Akeredolu ya karbi takardar shaidan cin zabe
Rotimi Akeredolu. Hoto daga @Vanguardngrnews/Dayo Johnson
Asali: Twitter

A yau, Talata, ne aka samu barkewar cece-kuce dangane da nadin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa hadimarsa, Lauretta Onochie, a matsayin kwamishinar zabe daga jihar Delta.

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: An bankado yadda aka rinka sayen kuri'a akan N1K zuwa N7K a zaben Ondo

Da yawan 'yan Najeriya na ganin cewa nadin Lauretta a matsayn kwamshina a hukumar zabe ta kasa (INEC) bai dace ba saboda kowa ya san 'yar gani kashenin jam'iyyar APC ce.

Yanzu haka mambobin jam'iyyar PDP, mai hamayya, a majalisar dattijai sun bukaci Buhari ya janye nadin Lauretta matukar da gaske ya na kishin dimokradiyya da son ganin an gudanar da adalci ga kowacce jam'iyya yayin zabe.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya assasa tubalin ginin jami'ar musulunci ta As-Salam Global University, Hadejia, mallakar kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iqamatis Sunnah, JIBWIS, jihar Jigawa.

Shugaban ƙasar da ministan sadarwa , Dakta Isa Pantami ya wakilta ya assasa tubalin ginin jami'ar a wurin taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164