Da duminsa: Sanata Yusha'u Anka ya rigamu gidan gaskiya

Da duminsa: Sanata Yusha'u Anka ya rigamu gidan gaskiya

- Tsohon Sanata lokacin mulkin Obasanjo ya mutu bayan jinya a asibitin Abuja

- Za'a yi jana'izarsa da Azahar a Masallacin tarayya yau Talata

- Marigayin ya yi mulki a PDP sannan ya koma ANPP bayan wa'adin farko

Wani tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Yusha'u Anka, ya rasu da safiyar Talata a wani asibiti a Abuja, The Punch ta ruwaito.

Anka ya rasu ne misalin karfe 1 na dare bayan fama da ciwon zuciya.

Ya rasu yana mai shekaru 70 a duniya.

Dan uwan mamacin, Sani Anka, wanda yayi hira da jaridar Punch, ya ce za'ayi jana'izarsa misalin karfe 1 na ranar a Masallacin kasa, dake Abuja.

Sanata Anka ya wakilci al'ummarsa tsakanin Yunin 1999 zuwa Mayun 2007.

An nada shi shugaban kwamitin majalisar dattawan kan dabi'u, harkokin wajen najeriya, da harkokin yan sanda.

Anka ya zama Sanata ne karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a 1999 amma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Nigeria Peoples Party ANPP a 2007.

KU KARANTA: Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Da duminsa: Sanata Yusha'u Anka ya rigamu gidan gaskiya
Credit: Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA NAN: SARS: IGP Adamu ya bayyana lokacin fara horar da sabon sashin 'yan sanda

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel